Yanzu-yanzu: Bayan tashin Bam na jiya a Saudiyya, an kai hari ofishin jakadancin kasar dake Hague

Yanzu-yanzu: Bayan tashin Bam na jiya a Saudiyya, an kai hari ofishin jakadancin kasar dake Hague

- Kasar Saudiyya na fuskantar hare-haren ta'addanci kwanakin nan

- A farko wani ya kusa da mota cikin harami, sannan harin Bam, sannan kuma harbe-harbe

- Gwamnatin kasar Saudiyya ba atyi tsokaci kan lamarin har yanzu ba

Hukumar yan sanda dake Hague, kasar Netherlands a ranar Alhamis, 11 ga Nuwamba, ta tabbatar da labarin cewa an yi harbe-harbe a ofishin jakadancin kasar Saudiyya.

Bayan samun labarin harbe-harben, jami'an tsaron garin inda kotun duniya ICC take sun garzaya cikin ginin kuma sun samu harsasai a kasa, tashar ABC News ta ruwaito.

Amma, a cewar kakakin hukumar yan sanda dake Hague, Steven van Santen, babu wanda aka kashe ko ya ji rauni.

Har yanzu, yan sanda basu san dalilin da yasa aka kai hari ofishin jakadancin Saudiyya ba.

KU KARANTA: Bayan lallasa APC a zabe, ana bikin rantsar da Godwin Obaseki wa'adi na 2 (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Bayan tashin Bam na jiya a Saudiyya, an kai hari ofishin jakadancin kasar dake Hague
Yanzu-yanzu: Bayan tashin Bam na jiya a Saudiyya, an kai hari ofishin jakadancin kasar dake Hague Credit: Daily Sabah
Asali: UGC

Mun kawo muku rahoton cewa an kai harin bam wajen da jami’an diflomasiyya na kasashen waje suka hadu don ranar tunawa da mutanen da suka mutu a yakin duniya ta daya.

Lamarin wanda ya afku a birnin Jiddah ta kasar Saudiyya ya yi sanadiyar jikkata mutane da dama.

A bisa ga wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin waje ta kasar Faransa, ta bayyana cewa bam din ya tashi ne a wata makabarta da ba ta Musulmi ba a yayin taron tunawa da mamatan, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Faransa ta yi Allah-wadai da lamarin wanda ta kira da “harin da matsorata suka kai da baya bisa ka’ida.”

KU KARANTA: Mun amince da komawar Gwamna Ebonyi APC, PDP ba tayi mana hallaci ba - Ohanaeze Ndigbo

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng