Bayan lallasa APC a zabe, ana bikin rantsar da Godwin Obaseki wa'adi na 2 (Hotuna)
- Bayan watanni biyu da lashe zabe, an rantsar da Godwin Obaseki karo na biyu
- Obaseki ya lallasa jam'iyyar APC a zabe kuma ya kafa tarihi a jihar
- Bikin rantsarwan ya samu halartan manyan jigogin PDP a yankin kudu
Bayan lallasa abokin hamayyarsa na jam'iyyar All Progressives Congress APC, Osaze Ize Iyamu a zaben ranar 19 ga Satumba, 2020, yau ake rantsar da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, wa'adi na biyu.
Manyan yan siyasa da jigogin jam'iyar Peoples Democratic Party PDP sun halarci taron.
Daga ciki akwai gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa; shugaban matatar man OPAC, Momoh Jimoh; gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike.
Bayan rantsarwan yau, Obaseki zai jagoranci al'ummar jihar daga 2020 zuwa 2024.
Kalli hotunan:
KU KARANTA: Bayan tashin Bam na jiya a Saudiyya, an kai hari ofishin jakadancin kasar dake Hague
KU KARANTA: Mun amince da komawar Gwamna Ebonyi APC, PDP ba tayi mana hallaci ba - Ohanaeze Ndigbo
Gwamna Godwin Obaseki ya lashe zabe karo na biyu karkashin jam'iyyar PDP a ranar 19 ga Satumba, 2020, kamar yadda INEC ta sanar.
A sakamakon da INEC ta saki, Godwin Obaseki ya samu kuri'u 307,955, yayinda abokin hamayyarsa, Osaze Iyamu, ya samu kuri'u 223,619.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng