Ba zamu iya cire rubutun larabcin dake cikin takardar Naira ba - CBN

Ba zamu iya cire rubutun larabcin dake cikin takardar Naira ba - CBN

- Lauya ya shigar da kara kotu domin bukatar cire rubutun ajami daga kan Naira

- Ya ce ana kokarin Musuluntar da Najeriya kuma hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya

Babban bankin Najeriya CBN ta nuna rashin amincewarta da karar da wani ya shigar babban kotun tarayya dake Legas na bukatar cire rubutun larabcin dake kan takardar kudin Najeriya 'Naira'.

Wani Lauya mazauni jihar Legas, Malcom Omirhobo, wanda ya shigar da kara gaban Alkali Mohammed Liman, ya ce rubutun yaren larabcin dake jikin Naira na nuna cewa Najeriya kasar Musulunci ce alhalin ba haka take a kundin tsarin mulki ba.

Lauyan, wanda yace shi bai san ma'anar rubutun ajamin ba, ya bukaci kotu ta cire kuma ta maye gurbin da na Turanci, ko kuma harsuna uku mafi shahara a Najeriya watau Hausa, Yoruba ko Igbo.

A cewar lauyan, da rubutun ajamin, CBN ta saba sashe 10 da 55 na kundin tsarin mulkin Najeriya, PUNCH ta ruwaito.

Amma a cewar lauyan CBN, yace "rubutun ajamin dake kan kudin Najeriya ba ya nufin wani addini ko hulda da larabawa."

Lauyan CBN ya caccaki lauyan kan ikirarin cewa rubutun ajamin barazana ce ga yancin addini a Najeriya.

"Rubutun dake kan takardar kudin kasar nan ba barazana bane ga kasa kuma bai sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya ba."

"Tun shekarar 1973 da aka canza kudin Najeriya daga Fam zuwa Naira ake amfani da rubutun Ajami."

"Rubutun Ajami ba alama bane na Musulunci, innama an yi ne domin saukakawa wadanda basu iya karatun Boko ba wajen kasuwanci," CBN tayi bayani.

KU KARANTA: Joe Biden: Muhimman abubuwa 7 da ya kamata ka sani kan zababben shugaban Amurka

Ba zamu iya cire rubutun larabcin dake cikin takardar Naira ba - CBN
Ba zamu iya cire rubutun larabcin dake cikin takardar Naira ba - CBN
Asali: Original

KU KARANTA: Wani dan shekara 69 ya yi ikirarin ya saki matarsa don ta zabi Joe Biden a zaben Amurka

CBN ya ce Najeriya za tayi asaran makudan kudi idan aka cire rubutun saboda za'a zubar da kudaden da aka riga aka wallafa.

Alkali Liman Mohammed zai saurari karan ranar Talata (Yau)

Hakazalika zai sake sauraron karar da wannan lauya dai ya shigar na cire rubutun larabcin dake jikin tambarin hukumar Sojin Najeriya.

Kamar CBN, hukumar Soji ta bukaci Alkalin yayi watsi da karar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel