Wani dan shekara 69 ya yi ikirarin ya saki matarsa don ta zabi Joe Biden a zaben Amurka

Wani dan shekara 69 ya yi ikirarin ya saki matarsa don ta zabi Joe Biden a zaben Amurka

- Wani dan kasar Amurka ya ce ya saki matarsa saboda ya gano da jefa wa Joe Biden kuri'a yayin zaben shugaban kasa na 2020

- Mutumin da ya yi ikirarin cewa shekarunsa 69 ya ce sun kwashe shekaru 30 suna zaman aure da matarsa amma ba zai iya cigaba da zama da ita ba

- Ya yi ikirarin cewa magudi aka tafka a zaben don haka zai tafi kasar Columbia kuma ba zai dawo ba har sai Amurka ta gyaru

Wani mutum mai shekaru 69 ya yi ikirarin cewa ya saki matarsa da suka kwashe shekaru 30 suna zaman aure kawai don ya gano ta zabi dan takarar jam'iyyar Democrat, Joe Biden a zaben shugaban Amurka na 2020.

Mutumin ya kuma yi ikirarin cewa zai tattara komatsansa ya yi hijira zuwa kasae Columbia kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter mai suna @Blanko_b7 kamar yadda LIB ta ruwaito.

Wani mutum ya yi ikirarin ya saki matarsa don ta zabi Joe Biden a zaben Amurka
Wani mutum ya yi ikirarin ya saki matarsa don ta zabi Joe Biden a zaben Amurka. Hoto daga @lindaikeji/ @Blanko_b7
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sanata Ladoja ya mayarwa Obasanjo martani kan batun tsige shi a matsayin gwamna a 2006

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke martani a kan rubutun da Joe Biden ya wallafa kan shirinsa na yaki da annobar Covid 19.

A cewarsa, ya gama saka hannu kan takardun raba auren kuma 'an kammala komai'. Ya kara da cewa ya yi takaicin ganin cewa sun yi shekaru 30 suna tare da matarsa.

KU KARANTA: Harin Musulmin Ƙabilar Igbo: MURIC ta buƙaci a gurfanar da Rev Fr. Onah

Har wa yau, ya kara da cewa ba zai dawo Amurka ba har sai an gyara kasar.

A wani labarin daban, mutanen garin Kungurki a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a Jihar Zamfara sun daƙile harin da ƴan bindiga suka kai musu a cewar rahoton Daily Trust.

Wasu ƴan garin sun ce ƴan bindigan sun kai musu hari ne sakamakon rashin jituwa da aka samu tsakanin wani mai shago da ɗan bindiga a garin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164