Joe Biden: Muhimman abubuwa 7 da ya kamata ka sani kan zababben shugaban Amurka

Joe Biden: Muhimman abubuwa 7 da ya kamata ka sani kan zababben shugaban Amurka

- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Democratic Party, Joe Biden ya yi nasara kan Shugaba Donal Trump a zaben 2020

- Tuni dai zababben shugaba Biden ya yi jawabinsa na godiya da Amurkawa kan zabensa inda ya yi alkawarin yi wa kowa adalci

An haifi Jospeh Biden Jr ne a ranar 20 ga watan Nuwamban 1942. Biden dan siyasar Amurka ne kuma zababben shugaban Amurka bayan ya yi nasara kan Shugaba Donald Trump a zaben shugaan kasa na 2020.

Za a rantsar da shi a matsayin shugaban Amurka na 46 a watan Janairun 2021.

Ga wasu muhimman abubuwa da ya kamata ka sani game da shi kamar yadda The Nation ta tattara.

Joe Biden: Muhimman abubuwa 7 da ya kamata ka sani kan zababben shugaban Amurka
Joe Biden: Muhimman abubuwa 7 da ya kamata ka sani kan zababben shugaban Amurka. Hoto: @JoeBiden
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: An yi wa 'yar gidan sarautar Saudiyya fashi

1. Biden dan jam'iyyar Democratic Party ne, a baya ya rike mukamin mataimakin shugaban Amurka na 47 daga 2009 zuwa 2017 sannnan ya rike mukamin sanata mai wakiltar Delaware daga 1973 zuwa 2009.

2. Ya girma ne a Scranton, Pennsylvania da New Castle County a Jihar Delaware.

3. Biden ya yi karatu a Jami'ar Delaware kafin daga bisani ya yi karatun digiri daga Jami'ar Syracuse a shekarar 1968.

KU KARANTA: Ba ku isa kuyi mana mulkin mallaka ba - Kungiyar Dattijan kudu ga gwamnonin Arewa

4. An zabe shi kansila na New Castle a 1970 ya kuma zama sanata mafi karancin shekaru na shida a tarihin Amurka a lokacin da aka zabe shi sanatan Amurka daga Delaware a 1972.

5. An zabi Biden a matsayin sanata har sau shida kuma shine sanata na hudu cikin wadanda suka fi yawan shekaru a majalisar a lokacin da ya yi murabus don ya zama mataimakin Shugaba Barack Obama.

6. A watan Afrilun 2019, Biden ya sanar da cewa zai yi takara kuma ya samu kuri'un wakilai da ya bashi damar zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Democratic Party a Yunin 2020.

7. Biden na mataimakin shugaban kasa na biyu a tarihin Amurka da ya zama zababben shugaban kasa bayan ya sauka daga mulki tun bayan Richard Nixon a shekarar 1968.

A wan rahoton, kungiyar malam jami'a (ASUU) a ranar Juma'a ta roki gwamnatin tarayya ta taji tausayin yayan talakawan Najeriya, ta kuma gaggauta amincewa da bukatar domin kuwa sun gaji da yajin aiki.

Kungiyar tace gwamnati na matsa mata akan ta janye yajin aikin ne, saboda ganin irin barnar da matasa suka yi lokacin zanga zangar Endsars kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel