Manyan 'yan siyasa sun hallarci ɗaurin auren ɗan Aliero da 'yar Yariman Bakura a Sokoto
- Sanatoci hudu da wasu sharararrun mutane sun kai ziyara Sokoto don halartar daurin aure
- An daura aure tsakanin yayan Sanatoci guda biyu, Injiniya Sulaiman Adamu dan gidan Sanata Adamu Aliero da amaryarsa Dr. Fatima Ahmed Sani yar gidan Sanata Ahmed Sani Yarima
- An daura auren a kan sadaki 100,000 a gidan yayan Yarima kuma sarkin Bakura, Alhaji Bello Ahmed Sani, a Mabera, Sokoto
Shugaban Majalisar Mattawa, Dr. Ahmad Lawan da shugaban masu rinjaye, Abdullahi Yahayya da wasu Sanatoci hudu sun ziyarci Sokoto don halartar bikin dan gidan Sanata Adamu Aliero, Injiniya Sulaiman Adamu.
Sulaiman ya auri yar gidan Sanata Ahmed Sani Yarima, Dakta Fatima Ahmed Sani.
An karkare daurin auren akan sadaki Naira 100,000.
DUBA WANNAN: An yi wa 'yar gidan sarautar Saudiyya fashi
An daura daura auren a gidan yayan Yarima kuma sarkin Bakura, Alhaji Bello Ahmed Sani, a Mabera, Sokoto.
Shugaban majalisar dattawan ne ya yi wa amarya Wali, yayin da gwamnan Zamfara, Alhaji Bello Matawalle, ya yi wallicin Ango.
Daga cikin manyan mutanen da suka halarci wannan aure akwai: Sanata Aliyu Magatakarda Wammako, Sanata Bala ibn Na'allah, Sanata Ibrahim Gobir da Sanata Danbaba Dambuwa.
KU KARANTA: Ba ku isa kuyi mana mulkin mallaka ba - Kungiyar Dattijan kudu ga gwamnonin Arewa
Daurin auren ya kuma samu halartar ministan harkokin 'yan sanda, Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi, da ministan Shari'a Abubakar Malami, SAN, da 'yan majalisu da dama na jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara.
Wakilin Najeriya a Tanzania, Amb. Sahabi Isa Gada, tsohon ministan sufuri, Alhaji Yusuf Suleiman, da kuma dan takarar gwamna a jam'iyyar APC Alhaji A. A. Gumbi duk sun halarci taron.
Gwamnonin Sokoto, Kebbi, Zamfara da Yobe, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, Senator Abubakar Atiku, Alhaji Bello Matawalle da Alhaji Mai-Mala Buni duk sun samu halartar daurin auren.
Anyi addu'o'in samun zaman lafiya ga auren da kuma kasa baki daya wanda Sheikh Bashir Gidan Kanawa ya jagoranta.
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, fitattun 'yan majalisa musulmai na Amurka duk sun ci zabensu a majalisar wakilai na tarayya yayin da wasu sabbi sun kuma yi nasarar lashe zabe a majalisun jihohi.
Musulmai 'yan kasar Amurka sun fito kwansu da kwarkwata sunyi zabe a cewar shahararren kungiyar kare hakokin musulmi a kasar, Council on American-Islamic Relations (CAIR).
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng