Ba ku isa kuyi mana mulkin mallaka ba - Kungiyar Dattijan kudu ga gwamnonin Arewa
- Kungiyar Dattijan kudu sun gargadi manyan Arewa cewa basu isa suyi musu mulkin mallaka ba
- Kamata yayi a hada kai a magance matsalar Kasar nan bawai ku dinga hangen wani abu daban ba
- Dole ne ayi kwaskwarima kafin zaben shugaban kasar 2023 a cewar SMBLF
Kungiyar dattijan kudu (SMBLF), ranar Laraba ta mayar da martani akan taron da gwamnoni da sarakuna da dattijan Arewa suka gudanar, tana cewa dattijan Arewa baza su yi musu mulkin mallaka ba.
Dattijan Kudun kuma sun ce dole ne a sake fasalin Najeriya kafin zaben shugaban kasar 2023.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Manyan Arewan sun gudanar da taron ne kwana Uku da suka wuce a Kaduna, inda suka bayyana cewa baza a raba kasar nan ba kuma zanga zangar #EndSARS da akayi a baya bayan nan yunkuri ne na lalata mulkin Buhari.
DUBA WANNAN: Alkali ya bada belin Naziru Sarkin Waƙa
Sun kuma goyi bayan gwamnatin tarayya kan shirinta na daidaita tsarin amfani da kafafen sadarwa.
Amma sai dai manyan kudu basu amince da matsayar gwamnonin Arewa ba. Su ka kara da cewa su fa baza a yi musu mulkin mallaka ba.
"Ba muga alamar tausayi ba akan yadda matasan Arewa ke murna da abin da ya faru ba, basu shiga zanga zangar #EndSARS ba, kamar Su ma basu saci kayayyakin gwamnati a dakin adana kayayyaki ba yadda sauran matasa suka yi a sauran bangarorin kasar nan, wanda yake nuni da cewa matsalar su iri daya ce. Amma maimakon mu magance matsalar, Wasu daga cikin mu suna wata magana ta daban," a cewar dattijan kudu.
KU KARANTA: Wani mutum ya yi barazanar kai coci kotu idan bata biya shi kuɗin baikonsa na shekaru 19 ba
Sunce ganin yadda ake bawa wani bangare fifiko a kasar nan dole akwai bukatar ayi kwaskwarima.
A wani labarin, hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na Jihar Kano ta sanar da cewa tana shirin daukan sabbin ma'aikata a kalla 700 don kara wa kan 2,500 da ta ke da su a jihar a halin yanzu.
Shugaban na KAROTA, Baffa Dan'agundi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke zantawa da 'yan jarida a ranar Laraba a jihar Kano.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng