An yi wa 'yar gidan sarautar Saudiyya fashi
- An yi kutse cikin gidan 'yar gidan sarautan Saudiyya da ke Faransa an yi mata sata
- An sace mata kayayyaki da kudinsu ya kai Euro 600,000 da suka hada da agogo, zinarai da gwala-gwalai, agogo da sauransu
- A halin yanzu an kwantar da ita a asibiti yayin da 'yan sanda suka fara bincike don gano wanda ya aikata wannan fashin
Barayi sun sace kaya masu tsada da kudinsu ya kai Euro 600,000 daga gidan 'yar gidan sarautar Saudiyya da ke kasar Faransa kamar yadda wani na kusa da masu bincike ya sanar a ranar Juma'a.
'Yar gidan sarautar mai shekaru 47 ba ta shiga gidan ba tun watan Agusta amma da shigar ta sai ta gano an ce mata jakkuna, agoguna, kayan ado na zinari da wasu tufafin da kudinsu ya kai Dallar Amurka 720,000.
Yar gidan sarautar da ba a bayyana sunanta ba ta fada wani yanayi kuma an garzaya da ita asibiti, kawo yanzu ba ta yi magana da 'yan sanda ba kamar yadda The Punch ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Ba ku isa kuyi mana mulkin mallaka ba - Kungiyar Dattijan kudu ga gwamnonin Arewa
Majiyar ta ce akwai alamun barayin ba su balle kofofin shiga gidan ba da ke kusa da wank Avenue George V a tsakiyar babban birnin kasar Faransa.
Kayayyakin da suka sace sun hada da jakunnan Hermes 30 da kudin kowanensu ya kama daga Euro 10,000 zuwa 30,000 da agogon Cartier, kayan ado da tufafi.
Masu bincike sun fara binciken kan lamarin a hukumance karkashin jagorancin sashi na musamman masu yaki da 'yan kungiyar bata gari na rundunar 'yan sandar kasar.
Jaridar Le Parisien ta ruwaito cewa babban wanda ake zargi da hannu cikin satar a yanzu wani mutum ne da ke zaune a gidan 'yar sarkin tun watan Agusta.
Akwai wasu karin mukullen gidan da ba a gani ba a cewar rahoton jaridar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng