An sake zaɓen sabbin 'yan majalisu musulmai a Amurka
- Musulmi sun samu karin kujerun majalisu yayin zaben shekarar 2020 a kasar Amurka
- Tsaffin 'yan majalisa musulmi na kasar suma duk sunyi nasarar zarcewa kan kujerunsu
- Wasu daga cikin sabbin 'yan majalisun sun hada da Iman Jodeh, Maure Turner da Madinah Wilson-Anton
Fitattun 'yan majalisa musulmai na Amurka duk sun ci zabensu a majalisar wakilai na tarayya yayin da wasu sabbi sun kuma yi nasarar lashe zabe a majalisun jihohi.
Musulmai 'yan kasar Amurka sun fito kwansu da kwarkwata sunyi zabe a cewar shahararren kungiyar kare hakokin musulmi a kasar, Council on American-Islamic Relations (CAIR).
Direktan CAIR na kasa Nihad Awad ya ce: "Kafafen labarai da 'yan takara sun fahimci karfin da al'ummar musulmi ke da shi ta hanyar amfani da kuri'unsu yayin zabuka da dama a kasar ciki har da zaben shugaban kasa."
DUBA WANNAN: Mutanen gari sun fatattaki 'yan bindigan da suka kai musu hari a Zamfara
A daren ranar Laraba, 'yan majalisu musulmai guda uku sun lashe zabensu na komawa majalisun wakilai a mazabunsu.
Yan majalisun sun hada da Ilhan Omar a mazabar Minnesota, Rachida Tlaib a mazabar Michigan da Andre Carson na mazabar Indiana. Dukkansu uku 'yan jam'iyyar Democrat ne.
Tlaib da Omar fitattun 'yan majalisa ne tare da Alexandria Ocasio-Cortez da Ayanna Pressley da ake yi wa lakabi da 'The Squad'.
Yan majalisun sun fita daban da saura 'yan jam'iyyarsu ta Democrats saboda amfani da kujerarsu wurin yaki da tsare-tsaren Shugaba Donald Trump da ba su amince da su ba.
KU KARANTA: Zaɓen Amurka: Magoya bayan Trump sunyi zanga-zanga a ofishin ƙidayar ƙuri'u ta Arizona
A majalisar jihar, Iman Jodeh, musulma 'yar asalin kasar Palestin ta lashe zabe a Colorado.
A Oklahoma, Maure Turner ta zama 'yar majalisa musulma na farko da ta lashe zabe yayin da Madinah Wilson-Anton ita ma ta zama ta farko a Delaware.
A Jihar Wisconsin, Samba Baldeh ya lashe zaben dan majalisar jiha yayin da a Florida, Christopher Benjamin ya lashe zabe shima, dukkansu 'yan jam'iyyar Democrats ne.
A cewar PEW, akwai musulmi miliyan 3.45 a Amurka wadda bai kai kashi daya cikin 100 na kasar ba. Mafi yawacinsu sun fi yawa ne a New York, Michigan, Illinois da California (TRT World).
A wani labarin, hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na Jihar Kano ta sanar da cewa tana shirin daukan sabbin ma'aikata a kalla 700 don kara wa kan 2,500 da ta ke da su a jihar a halin yanzu.
Shugaban na KAROTA, Baffa Dan'agundi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke zantawa da 'yan jarida a ranar Laraba a jihar Kano.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng