Mutanen gari sun fatattaki 'yan bindigan da suka kai musu hari a Zamfara

Mutanen gari sun fatattaki 'yan bindigan da suka kai musu hari a Zamfara

- An yi artabu da tsakanin mazauna garin Kungurki da ƴan bindiga a Jihar Zamfara

- Lamarin ya faru ne sakamakon rashin jituwa da aka samu tsakanin wani mai shago da ɗan bindiga

- Sakamakon haka mazauna ƙauyen biyu sun mutu inda ɗan bindiga guda ɗaya shima ya mutu

Mutanen garin Kungurki a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a Jihar Zamfara sun daƙile harin da ƴan bindiga suka kai musu a cewar rahoton Daily Trust.

Wasu ƴan garin sun ce ƴan bindigan sun kai musu hari ne sakamakon rashin jituwa da aka samu tsakanin wani mai shago da ɗan bindiga a garin.

Mutanen gari sun 'fatattaki' 'yan bindigan da suka kai musu hari a Zamfara
Mutanen gari sun 'fatattaki' 'yan bindigan da suka kai musu hari a Zamfara. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Ba ku isa kuyi mana mulkin mallaka ba - Kungiyar Dattijan kudu ga gwamnonin Arewa

"Wasu ƴan bindiga sun isa garin ɗaya daga cikinsu ya shiga shagon wani mutum yana amsa waya.

"Mai shagon ya bukaci ɗan bindigan ya fice masa daga shago ko kuma ya yi maganinsa.

"Ɗan bindigan ya ƙi fita hakan yasa mai shagon ya ɗauki sanda ya doki ƴan bindigan.

"Hakan ya ɓata wa sauran ƴan bindigan da suke tare da mutumin rai.

"Sun koma baya suka sake shiri suka dawo da bindigu suna harbe harbe.

KU KARANTA: Zaben Amurka cike ya ke da magudi, ya kamata mu basu hayar shugaban INEC - Tsohon dan takarar shugaban kasa, Adamu

"An kashe ɗan bindiga ɗaya da mutanen ƙauyen biyu.

"Amma, an tura jami'an tsaro zuwa unguwar don dawo da zaman lafiya," a cewar mazaunin garin.

Anyi ƙoƙarin ji ta bakin kakakin ƴan sandan Jihar SP Muhammad Shehu amma hakan ya ci tura.

A wani labarin, hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na Jihar Kano ta sanar da cewa tana shirin daukan sabbin ma'aikata a kalla 700 don kara wa kan 2,500 da ta ke da su a jihar a halin yanzu.

Shugaban na KAROTA, Baffa Dan'agundi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke zantawa da 'yan jarida a ranar Laraba a jihar Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel