Za a ɗauki sabbin jami'an KAROTA 700 a Kano

Za a ɗauki sabbin jami'an KAROTA 700 a Kano

- Hukumar ta KAROTA ta jihar Kano ta ce za ta dauki sabbin ma'aikata guda 700

- Hukumar ta ce za a tura sabbin ma'aikatan zuwa masarautun Bichi, Rano, Karaye da Gaya

- Har wa yau, hukumar ta gargadi al'umma su guji yin talla a wuraren da ba a halasta yin hakan ba

Hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na Jihar Kano ta sanar da cewa tana shirin daukan sabbin ma'aikata a kalla 700 don kara wa kan 2,500 da ta ke da su a jihar a halin yanzu.

Shugaban na KAROTA, Baffa Dan'agundi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke zantawa da 'yan jarida a ranar Laraba a jihar Kano.

A cewarsa, za a tura sabbin jami'an da za a dauka zuwa masarautun Bichi, Rano, Karaye da Gaya a jihar.

Mista Dan'agundi ya ce za a tura jami'an zuwa masarautun ne don tabbatar da bin dokokin tuki.

KAROTA za ta dauki sabbin ma'aikata 700 a Kano
Shugaban KAROTA, Baffa Dan'agundi. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yajin aiki: Iyayen ɗalibai za su' ji a jikinsu' idan ba mu yi nasara ba - ASUU

Shugaban ya kuma yi gargadi kan yin talla a wuraren da aka hana yin tallar inda ya ce duk wanda aka samu yana karya dokar zai fuskanci fushin hukuma.

Ya ce, "Mun saka dokoki masu tsauri don tabbatar da wadanda aka hana yin talla ba su dawo ba don irin wahalhalun da suke janyo wa masu amfani da titi."

Shugaban ya kuma ce nan gaba KAROTA za ta yi hadin gwiwa da Hukumar Kula da Tituna na Kano, KARMA, don yin gyare-gyaren tituna a jihar.

KU KARANTA: 'Yan shi'a sun ƙona tutar Faransa a Abuja kan kalaman shugaban Faransa, Macron

"Za muyi hadin gwiwa da KARMA don magance matsalar ramuka da ke tituna.

"Akwai wasu wuraren da ke bukatar gyare-gyare a tituna da ke bukatar mu bada gudunmawa wurin aikin.

"Za mu iya bada gudunmawar mu wurin saukaka cinkoso a hanyoyin," in ji shi.

A wani labarin daban, fusatattun matasa a garin Daudu a ƙaramar hukumar Gina, a ranar Talata, sun ƙona Divine Shadow Church kan alaƙanta mai cocin da satar mazakuta a garin kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kwana ki uku da suka shuɗe, matasan sun yi zanga zanga a babban titin Makurdi - Lafia kan abinda suka kira 'batar mazakutar' mutum shida cikin wata guda a garin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164