Zaɓen Amurka: Magoya bayan Trump sunyi zanga-zanga a ofishin ƙidayar ƙuri'u ta Arizona

Zaɓen Amurka: Magoya bayan Trump sunyi zanga-zanga a ofishin ƙidayar ƙuri'u ta Arizona

- Magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyar Republican, Donald Trump sun yi zanga-zanga a Arizona

- Masu zanga-zangar sun yi wa ofishin ƙidaya na jihar zobe ɗauke da rubutu da ke nuna ƙin amincewarsu da ƙidayar

- Wasu daga cikinsu suna ta maganganu da ke iƙirarin cewa ƴan Democrats suna tafka maguɗi wurin ƙidayar

Magoya bayan shugaban Amurka, Donald Trump, cikinsu ana zargin wasu na ɗauke da bindigu, sun zagaye ofishin zaɓe na Maricopa County da ke Arizona suna zanga-zanga kan zabe.

Wani bidiyo da aka nuna a CNN, ya nuna magoya bayan Trump ɗauke da saƙonni da ke nuna rashin jin daɗinsu kan hasashen da ke nuna jam'iyyar Democrats za ta yi nasarar cin kwallejin zaɓe 11 a jihar.

Zaɓen Amurka: Magoya bayan Trump sunyi zanga-zanga wurin ƙidayar ƙuri'u ta Arizona
Zaɓen Amurka: Magoya bayan Trump sunyi zanga-zanga wurin ƙidayar ƙuri'u ta Arizona. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mattacen ɗan takara da korona ta kashe ya ci zaben majalisa a Amurka

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Joe Biden wadda shine ɗan takarar jam'iyyar Democrat shine a kan gaba a Arizona duk da cewa tazarar ba yawa.

Kwamitin yaƙin neman zaɓe na Trump a daren ranar zaɓe sunyi watsi da rahotannin cewa sun sha kaye a jihar inda suka ce akwai ƙuri'u na wasiƙa da ba a ƙirga ba tukuna.

"Wane ke duba ƙuri'un wasika?" Kamar yadda aka jiyo wani mai zanga zanga na tambaya da na'urar amsa kuwwa a wani bidiyo da wakilin BBC Gadi Schwartz ya wallafa a Twitter.

"Democrats ne," a cewar amsar da wata mata ta bada. "Democrats ne ke duba su."

KU KARANTA: Alkali ya bada belin Naziru Sarkin Waƙa

A halin yanzu Biden ya bawa Trump tazara da kimanin ƙuri'u 80,000 a jihar kamar yadda The Associated Press ta ruwaito.

A daren Laraba, jihar ta ƙidaya ƙuri'u fiye da 300,000 a cewar rahoton Washington Post.

Tuni dai Trump ya wallafa wani bidiyo a shafukan sada zumunta inda ya ke iƙirarin cewa Democrats ne satar ƙuri'u.

A wani labarin, kungiyar malaman Jami'a (ASUU) ta ce kada iyaye su yi tunanin cewa abin da suke nema ya yi yawa da har zai sa su dauki dogon lokaci suna yajin aiki.

Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar ta bayyana cewa iyaye su lura cewa idan gwagwarmayarsu ta tashi a banza, "aljihun su zai koka wajen tura yaran su karatu jami'a."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel