Ku rabar da duk tallafin korona da ke jibge a manyan shaguna a fadin Najeriya - NLC ga FG, Jihohi

Ku rabar da duk tallafin korona da ke jibge a manyan shaguna a fadin Najeriya - NLC ga FG, Jihohi

- Fusatattun batagarin matasa sun cigaba da balle manyan shagunan ajiya na gwamnati tare da kwashe kayan abinci

- A makon da ya gabata ne matasa suka fara balle wani babban shagon gwamnati a jihar Legas tare da yin awon gaba da kayan tallafin korona dake ciki

- Tun bayan lokacin ake samun rahotannin balle manyan shagunan da aka ajiye kayan tallafin korona tare da kwashesu a sassan Najeriya

Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta bukaci gwamnatin tarayya da na jihohi su gaggauta rabar da duk wani sauran kayan tallafin korona da ke suka jibge a manyan shagunan ajiya da ke fadin kasar nan.

Kazalika, NLC ta yi Alla-wadai da barnatar da kayan tallafin korona da wasu batagari ke yi har yanzu a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi da NLC ta fitar ranar Litinin mai taken, 'NLC ta bukaci a gaggauta raba duk wasu kayan tallafin korona da sauran kayan agaji'.

DUBA WANNAN: Ku guji cin abinci da magungunan da aka sata a Kaduna, suna dauke da guba - NAFDAC ta yi gargadi

A cikin jawabin mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na kasa, Kwamred Ayuba Wabba, NLC ta ce; 'raba kayan zai taimakawa gwamnati wajen rage kuncin rayuwa da jama'ar ke ciki a halin yanzu'.

"A bayyane take cewa wasu jami'an gwamnati sun boye kayan tallafin korona da aka bayar domin a karshe su karkatar dasu.

Ku rabar da duk tallafin korona da ke jibge a manyan shaguna a fadin Najeriya - NLC ga FG, Jihohi
Shugaban NLC; Ayuba Wabba
Asali: Depositphotos

"An bayar da kayan ne domin a gaggauta rabawa mutane lokacin da aka saka dokar kulle bayan bullar annobar korona.

DUBA WANNAN: Zanga-zanga: FG ta ci tarar manyan gidajen talabiijin uku saboda kunyata gwamnati

"Babu wanda ya bayyanawa jama'a dalilin kin raba musu kayan tallafin korona. Wasu daga cikin kayayyakin sun fara lalacewa sakamakon dadewar da suka yi a jibge a shagunan ajiya.

"A yayin da muke Alla-wadai da barnata kayan tallafin korona da sauran kayan agaji da aka ajiye, muna ma su nuna kyamar halayen jami'an gwamnati da suka jibge wadannan kayayyaki da aka bayar domin rabawa talakawa a lokacin da suke cikin wahala da kunci.

"Mu na kira ga gwamnatin tarayya a kan ta binciki wadannan jami'ai tare da gaggauta rabar da sauran kayan tallafin korona da suka rage domin ragewa jama'a zafin halin wahalar rayuwa da suke ciki," a cewar jawabin NLC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel