Bata gari sun kai farmaki cibiyar killace masu korona a Jalingo, sun yashe komai harda gadaje

Bata gari sun kai farmaki cibiyar killace masu korona a Jalingo, sun yashe komai harda gadaje

- Fusatattun matasa sun kai mamaya cibiyar killace masu cutar korona a garin Jaligo

- Sun sace gadaje, katifu da sauran kayayyakin da ke cibiyar

- A yanzu haka an tattaro cewa cibiyar ta zama wayam babu komai a ciki

Wasu da ake zaton bata gari ne sun kai farmaki cibiyar killace masu cutar korona a Jalingo, babbar birnin jihar Taraba, sannan suka tafi da katifu da sauran kayayyakin da ke cibiyar.

Dubban matasa ne suka kai wa cibiyar wanda ke a sansanin NYCS, hanyar Wukari – Jalingo farmaki, inda suka fasa kofofin cibiyar.

An tattaro cewa yan iskan sun sace dukkanin katifu kimanin guda 200 da sauran kayayyaki.

KU KARANTA KUMA: An kashe mutum 1 yayinda bata gari suka yi yunkurin kona ofishin yan sanda a Ibadan

Bata gari sun kai farmaki cibiyar killace masu korona a Jalingo, sun yashe komai harda gadaje
Bata gari sun kai farmaki cibiyar killace masu korona a Jalingo, sun yashe komai harda gadaje Hoto: Healthwise
Asali: UGC

Tawagar hadin gwiwa na yan sanda da sojoji da aka tura wajen domin hana matasan satar kayayyakin cibiyar sun gaza yin komai don dakatar da su.

An gano bata garindauke da kayayyakin da suka sace a kawunansu yayinda wasu suka yi amfani da adaidaita sahu wajen kwasar nasu kayayyakin na sata zuwa kauyukan da ke makwabtaka da garin Jalingo.

Wani idon shaida ya bayyana cewa cibiyar ya zama wayam babu komai kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: An kuma: Bata gari sun ɓalle daƙin ajiyar abinci a Abuja, sun kwashe komai

A gefe guda, Jama’a da ke yawon neman wajen da aka ajiye kayan tallafin korona sun kai farmaki wani rumbun ajiye kaya a Gwagwalada, babbar birnin tarayya, Abuja.

Kayayyakin da suka sace sun hada da shinkafa, semovita, taliya, siga, gishiri da taki.

Rumbun ajiyar wanda ke kusa da ofishin WAEC, an tattaro cewa yana dauke da kayayyaki mallakar hukumar birnin tarayya.

A ranar Lahadi na wasu matasa sun fasa wani rumbun ajiya a yankin Jabi kuda da kotun kula da da’ar ma’aikata.

Ba tare da duba kasancewar sojoji da yan sanda a wajen ba, matasan sun yashe kayayyaki daban-daban da aka ajiye a rumbun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel