Buhari ya gana da GEJ, Bagudu, Badaru da Buni a Villa

Buhari ya gana da GEJ, Bagudu, Badaru da Buni a Villa

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin manyan baki a fadarsa ranar Alhamis

- Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya ziyarci shugaba Buhari domin gabatar masa da rahoto a kan rikicin kasar Mali

- Kazalika, shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamnonin jam'iyyar APC uku; Atiku Bagudu, Badaru Abubakar, da Mai Mala Buni

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, wanda yakai masa ziyara domin gabatar masa da rahoto a kan rikicin kasar Mali.

Kazalika,shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da gwamnonin jihohin; uku na jihar Kebbi, Atiku Bagudu, na jihar Jigawa, Badaru Abubakar, da na jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Ya zuwa yanzu babu wani jawabi da fadar shugaban kasa ko gwamnonin suka fitar dangane da dalilin ganawarsu da Buhari.

DUBA WANNAN: Sharaf-sharaf da hawaye: Bidiyon yadda matashi ya ci kuka bayan an ragargaje motarsa a wurin zanga-zanga

Buhari ya gana da GEJ, Bagudu, Badaru da Buni a Villa
Buhari yayin ganawa da GEJ
Asali: Twitter

Buhari ya gana da GEJ, Bagudu, Badaru da Buni a Villa
Buhari da Bagudu a Villa
Asali: Twitter

Buhari ya gana da GEJ, Bagudu, Badaru da Buni a Villa
Buhari da Badaru a Villa
Asali: Twitter

Buhari ya gana da GEJ, Bagudu, Badaru da Buni a Villa
Buhari yayin ganawa da Bagudu, Badaru da Buni a Villa
Asali: Twitter

Legit.ng Hausa ta wallafa cewa a ranar Talata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara shirin ruguza hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da dangoginsu da suka hada da EFCC da kuma ICPC.

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar shugaba Buhari a zauren majalisar, mai taken: "Dokar hukumar gurbattun kudade".

Ahmad Lawan ya ce sabuwar dokar za ta magance matsalar rufa rufa da ake yi wajen alkinta kudaden da hukumomin biyu ke kwatowa daga barayin kasa.

Buhari a cikin wasikar ya bayyana cewa aikewa majalisar dattijai bukatar rushe hukumomin da samar da sabuwar dokar ya samu sahalewar majalisar zartaswa ta kasa.

DUBA WANNAN: Ethiopia ta yi murnar shiga sabuwar shekarar 2013 a yayin da kasashen duniya ke hangen 2021

A cewar wasikar da aka aikata a ranar 6 ga watan Oktoba, sabuwar dokar hukumar zai tabbatar da yaki da cin hanci da rashawa, safarar kudade ba bisa ka'ida ba da sauran laifuka.

"Muhimmancin dokar shine kirkirar hukumar yaki da gurbatattun kudade (alkinta kudaden da aka kwato).

"Manufofin hukumar shine sa ido kan dokar da kuma yin ruwa da tsaki a alkinta kudaden da aka kwato daga barayin kasa ta hanyar hadin kai da hukumomin tsaro.

"Sannan abu mai muhimmanci shine, hukumar za ta tabbata 'yan Nigeria sun amfana da kudaden da aka kwato daga mahandaman kasar, ba tare da boye boye ba."

Idan har aka amince da wannan doka, za ta taimaka wajen dakatar da EFCC da sauran hukumomin yaki da rashawa guda 6 daga rufe asusun mutanen da ake bincika.

Sauran hukumomin sun hada da hukumar ICPC, NDLEA, NFIU, NAPTIP, CCB da kuma rundunar 'yan sandan Nigeria," a cewar shugaban majalisar dattijan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel