Na taba kwasar kashina a hannun 'yan sanda - Mataimakin gwmanan Oyo

Na taba kwasar kashina a hannun 'yan sanda - Mataimakin gwmanan Oyo

Mataimakin gwamnan jihar Oyo, Rauf Olaniyan ya tabbatar da rashin imani da cin zarafin da ake zargin jami'an rundunar 'yan sanda na SARS su ke yi wa jama'a.

Olaniyan, wanda ya shiga sahun dubunnan masu zanga zanga a kofar shiga babbar sakatariyar gwamnatin jihar Oyo, Agodi Ibadan, ya yi kira da a kawo karshen zaluncin 'yan sanda.

Mataimakin gwamnan, wanda ya shiga sahun masu zanga zangar yana dauke da allon kwali a kofar shiga sakatariyar, ya ce sau biyu jami'an SARS suna cin zarafin sa.

KARANTA WANNAN: IGP ya gayyaci jami'an SARS Abuja domin ayi masu gwajin kwakwalwa

Na taba kwasar kashina a hannun 'yan sanda - Mataimakin gwmanan Oyo
Na taba kwasar kashina a hannun 'yan sanda - Mataimakin gwmanan Oyo - @Reporters_Large
Asali: Twitter

Rubutun da ke jikin allon kwalinsa na cewa: "Sau biyu jami'an 'yan sanda suna cin zarafina, Rauf Olaniyan.

“#EndPoliceBrutalityNow, #ReformNigerianPoliceNow”

A wani labarin, Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda, Mohammed Adamu a ranar Talata ya umurci gaba daya jami'an da ke a sashen dakile fashi da makami SARS da su je shelkwatar rundunar da ke Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an idan sun je Abuja, za ayi masu gwajin kwakwalwa a shirye shiryen yi masu horo don rarrabasu zuwa wasu sashe sashe na rundunar.

A wani ci gaban, IGP ya samar da sashen jami'an da suka kware a sarrafa makamai da fada (SWAT) da zai cike gurbin korarren sashen jami'an SARS.

Mambobin wannan sabon sashen za su samu horo da kuma jarabawar kwakwalwa domin tabbatar da cewa za su iya gudanar da wannan muhimmin aiki.

KARANTA WANNAN: Rundunar 'yan sandan Lagos ta kwace makamai daga hannun jami'an SARS

Za su fara samun horo a sansanonin horar da jami'an rundunar 'yan sanda daban daban da ke fadin kasar, a mako mai zuwa.

Za a horas da jami'an rundunar da ke a shiyyoyin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu a sansanin horas da jami'an na Nonwa-Tai, jihar Rivers.

Haka zalika, za a horas da jami'an rundunar 'yan sandan shiyyar Arewa da Kudu maso Yamma a kwalejin horas da 'yan sandan sintiri da ke Ende, jihar Nasarawa da kuma wacce ke Ila-Orangun, jihar Osun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel