Tauraro ya bada labarin cin kashin da aka yi masa a kungiyar Barcelona

Tauraro ya bada labarin cin kashin da aka yi masa a kungiyar Barcelona

- Luis Suarez ya bada labarin kwanakinsa na karshe a Kungiyar Barcelona

- ‘Dan wasan gaban ya ce an kai an daina barinsa ya yi atisaye da ‘yan wasa

- Suarez ya ce dole ta sa wulakancin da aka yi masa ya fusata Lionel Messi

‘Dan wasan kwallon kafa Luis Suarez ya fito ya bayyana cewa sai da ya yi kuka a game da yadda Barcelona ta yi waje da shi a watan Satumban nan.

Luis Suarez wanda ya bar kungiyar Barcelona ya koma Atletico Madrid a watan jiya, ya ce an kai lokacin da aka hana shi atisaye kafin ya bar kungiyar.

‘Dan kwallon ya ke cewa bai yi mamakin ganin yadda Lionel Messi ya tashi ya tsaya masa ba, a lokacin da ya fito fili ya rika caccakar manyan kulob din.

KU KARANTA: Lionel Messi ya yi kaca-kaca da Barcelona kan tashin Luis Suarez

“Akwai hanyoyin da za su iya fada mani cewa su na neman abubuwa su canza zani.” Inji Suarez bayan ya zura kwallo a wasan Uruguay da Chile jiya.

‘Dan wasan ya ce: “Yadda su ka yi mani, ka na jin cewa kamar ana neman kai da kai, shi ne ya fi yi mani ciwo sosai. Wadannan kwanaki ba su yi mani dadi ba.”

Tauraron ya ke fadawa ‘yan jarida: “Sai da na yi kuka a kana bin da ya ke faruwa da ni.”

Tsohon kwallon na Liverpool ya ce yadda aka kora shi daga kulob din ya masa ciwo, amma ya ce ya zama dole mutum ya fahimci cewa Duniya juyi-juyi ce.

KU KARANTA: Luiz Suarez ya yarda ya koma Atletico

Tauraro ya bada labarin cin kashin da aka yi masa a kungiyar Barcelona
Luis Suarez Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

‘Dan kwallon ya ce abin da aka yi masa, ya yi wa Messi ciwo, kuma har mai dakinsa ta lura da yadda ya zama, dole da Atletico su ka zo, ya yi maza ya tafi.

“Akwai abin da mutane ba su sani ba, amma ka je wasa a Barcelona, sai a kora ka, ka yi atisaye kai kadai, domin ba za ayi kwallo da kai ba.” Ya ce ba dadi.

Kun ji cewa duk da Suarez ya ci wa Barcelona kwallaye 198 – ya zama ‘dan wasa na uku a jerin wadanda su ka fi kowa kwallaye a tarihi, an yi waje da shi.

Sabon Kocin da aka dauko, Ronald Koeman ya shaidawa ‘Dan wasan tashi ta kare a Barcelona.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel