Yadda satar garin tuwo ta tilasta ba da katin shaida a wurin nika a Kano

Yadda satar garin tuwo ta tilasta ba da katin shaida a wurin nika a Kano

- Mazauna wasu unguwanni na fama da korafi a kan sace-sacen garin tuwo da ake masu a wajen nika a birnin Kano

- Faruwar wannan al'amari ta tilasta ba da katin shaida a wurin nika

- Sai dai an danganta wannan lamari da halin da talaka ya tsinci kansa a ciki na matsayin rayuwa da tsadar kayan masarufi

A yayinda talakawa ke ci gaba da kukan babu da matsin rayuwa, mazauna wasu unguwanni a birnin Kano, na korafi a kan yadda ake sace masu garin tuwonsu a wajen nika a yan kwanakin nan.

A lokutan baya da wuya ka ji an ce an sace garin tuwo a wurin nika sai dai a samu yanayin da ake yin musaya bisa kuskure, wato wani ya dauki na wani.

An tattaro cewa wannan sabon sauyi da aka samu na sace-sacen garin ya sanya wasu masu injin nika sun fara ba da katin shaida domin rage afkuwar hakan.

A yanzu idan mutum ya kai nika, sai a bashi katin shaidar cewa ya kai nika wajen.

KU KARANTA KUMA: Buhari ba shi da ikon sauya fasalin tsarin mulkin Najeriya - Tanko Yakasai

Yadda satar garin tuwo ta tilasta ba da katin shaida a wurin nika a Kano
Yadda satar garin tuwo ta tilasta ba da katin shaida a wurin nika a Kano Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da wani rahoton Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, ya ce an samu karin mutum fiye da miliyan guda da ke fama da karancin abinci a jihar Kano sakamakon annobar korona, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Sai dai kuma, mutane da dama na danganta al'amarin da irin matsin rayuwar da jama'a suka samu kansu a ciki saboda tashin gwauron zabi da farashin kayan masarufi ya yi.

An dai samu tashin farashin kayayyaki sakamakon karin kudin man fetur da wutar lantarki da gwamnatin Najeriya ta yi.

KU KARANTA KUMA: Garambawul: Dattawan arewa sun mara wa Adeboye baya, sun yi korafi cewa Najeriya ta gaza

A wani labarin, kimanin iyalai 12,100 da kuma masu kananan sana'o'i na jihar Kano zasu amfana da tallafin COVID-19 a jihar, a cewar wakilin UNDP Muhammad Yahaya.

Kamar yadda wakilin UNDP, Muhammad Yahaya ya bayyana, an bada wannan tallafin ne don taimakon 'yan jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel