Jawabin rabuwar Najeriya: Dattawan Arewa sun gargadi mataimakin shugaban kasa Osinbajo

Jawabin rabuwar Najeriya: Dattawan Arewa sun gargadi mataimakin shugaban kasa Osinbajo

- Kungiyar dattawan Arewa ta gargadi mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo kan kalaman da ya yi na cewa Najerya za ta iya ruguje wa

- Kungiyar dattawan ta amince akwai matsaloli a kasar amma ta ce ta yi imanin kasar za ta iya warware su kamar yadda ta yi a baya

- Don haka ta gargadi Osinbajo da sauran shugabanni su rika fadin kalaman da za su kwantar da hankula da hada kan mutane ba akasin haka ba

Ka iya bakin ka: ACF ta yi wa Osinbajo gargadi kan batun rabuwar Najeriya
Ka iya bakin ka: ACF ta yi wa Osinbajo gargadi kan batun rabuwar Najeriya. Hoto: @SaharaReporters
Asali: Twitter

Kungiyar dattawan arewa, ACF, ta soki mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a kan jawabin da ya yi na cewa rabuwar kan da aka samu a Najeriya a yanzu zai iya sanadin rabuwar kasar.

A yayin da kungiyar ta amince akwai rabuwar kai a Najeriya, ta ce bai dace mataimakin shugaban kasar ya rika fadin kalaman da za su kara janyo tabarbarewar lamarin ba.

DUBA WANNAN: Mutum 30 sun mutu a harin da ISWAP ta kai wa tawagar gwamnan Borno

ACF din ta gargadi Osinbajo akan furta kalaman da za su kara tada hankali a kasar.

Osinbajo wanda sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya wakilta a wani taron coci da aka yi a ranar Lahadi a Abuja don murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yanci ya ce, "Katangan mu bai rushe ba tukunna, amma akwai wuraren da suka tsage kuma idan ba gyarawa aka yi ba za ta rushe."

Sakataren gwamnatin tarayyar ne ya karanto jawabin na Osinbajo a wurin taron.

KU KARANTA: Zargin barazana ga rayuwa: IMN ta yi wa jarumin da ya Pete Edochie martani

Kungiyar ta arewa ta amince akwai baraka a kasar amma ta ce kasar za ta farfado ta dinke barakar.

A hirar da ya yi da The Punch, Sakataren watsa labarai na ACF, Emmanuel Yawe yayin da ya ke martani a kan jawabin na mataimakin shugaban kasa ya gargadi sauran shugabanin kasar su 'kula da irin abinda suke fadi'.

Kakakin na ACF cikin hirar ya ce, "Akwai baraka amma muna tsamanin mataimakin shugaban kasar ya kwantar da hankulan mutane ne ba ya fadi abinda zai harzuka su ba.

"ACF tana fatan cewa Najeriya za ta magance matsalolin da suke addabar ta kamar yadda ta yi a baya don kare abinda zai janyo ta ruguje. Domin cimma hakan, Shugabannin Najeriya irinsu Osinbajo su kula da abinda ke fitowa daga bakinsu."

A wani rahoton daban, kun ji Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya lashe kyautar Zik a rukunin shugabanci na shekarar 2019 kamar yadda Farfesa Pat Utomi ya sanar a ranar Alhamis.

Zulum wanda shine mutum na takwas cikin jerin wadanda suka lashe kyautar an karrama shi ne saboda shugabanci na gari. Read more:

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel