Akwai yiwuwar shiga wahalar fetur bayan ma’aikatan motoci sun shiga yaji

Akwai yiwuwar shiga wahalar fetur bayan ma’aikatan motoci sun shiga yaji

- Direbobin motocin haya sun ce za su fara sabon yajin aiki a yau dinnan

- Shugaban NARTO ya bayyana cewa a yau ne za shiga yajin jan-kunne

- Bayan nan Direbobi za su dauke kafa idan har ba a dauki wani mataki ba

A ranar Litinin, 21 ga watan Satumba, 2020, kungiyar NARTO ta direbobinn motocin Najeriya, ta bada sanarwar za ta shiga yajin aiki a yau Talata.

Kungiyar direbobin su na da hannu wajen jigilar mai da fasinjoji da kuma kaya a kan hanyoyin Najeriya da kuma sauran kasashen Afrika ta yamma.

Shugaban NARTO na kasa, Alhaji Yusuf Lawal Othman, ya zanta da manema labarai jiya, inda ya shaida masu dalilinsu na tafiya wannan yajin aiki.

KU KARANTA: Mun daina tsaida farashin mai a Najeriya - PPPRA

Da ya ke magana da ‘yan jarida a garin Abuja, Yusuf Lawal Othman, ya ce direbobin motocin haya sun yi mamakin jin labarin hana su bi ta kan tituna.

Jaridar The Nation ta rahoto NARTO ta na kokawa da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na haramtawa motoci masu cin lita sama da 45, 000 bin titi.

Shugaban kungiyar ya ce su fara yajin aiki a yau, 22 ga watan Satumba, 2020, domin su ja kunnen gwamnati. NARTO ta ce za ta bada wa’adin kwanaki 10.

Da zarar wannan wa’adi ya cika, kungiyar za ta janye aiki gaba daya har sai baba ta gani. Wannan wa’adi zai fara aiki ne daga ranar 24 ga watan Satumba.

KU KARANTA: NLC ta yi magana game da karin farashin fetur

Akwai yiwuwar shiga wahalar fetur bayan ma’aikatan motoci sun shiga yaji
Ministan harkokin mai, Timipre Sylva
Asali: UGC

Idan wannan ya faru, mutane da-dama za su rasa hanyar cin abinci, wannan ya sa tun farko kungiyar ta ja-kunnen gwamnatin Najeriya ta dauki mataki.

A cewar Alhaji Yusuf Othman, akwai rashin tausayi da rashin sanin ya kamata a matakin hana masu manyan motoci bin kan tituna duk da kokarin da su ke yi.

NARTO ta ce ta na taka rawar gani wajen kasuwanci da jigilar mai tsakanin jihohin kasar nan.

Kwanakin baya aka yi karin farashin mai, amma duk da haka Lai Mohammed ya ce babu kasar da ta kai Najeriya arahar man fetur a kaf Nahiyar Afrika har gobe.

Ministan ya tunawa jama'a cewa an yi lokutan da jama'a su ke daukar tsawon sa'o'i su na jiran layi ya zo kansu domin su saye fetur, ya ce wannan ya zo karshe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel