Bidiyo: Sojoji sun tarwatsa mafakan shugabannin 'yan bindiga Damina da Sani Mochoko a dajin Kuyambana a Zamfara

Bidiyo: Sojoji sun tarwatsa mafakan shugabannin 'yan bindiga Damina da Sani Mochoko a dajin Kuyambana a Zamfara

- Sojojin saman Najeriya sun yi nasarar lalata wasu gine ginen yan bindiga a dajin Kuyambana da ke jihar Zamfara

- Sojojin sun kai harin ne bayan samun ingantattun bayannan sirri da ke nuna cewa wasu hatsabibin shugabannin yan bindiga na amfani da wuraren a matsayin mafaka

- Sojojin sun yi luguden wuta a gine-ginen tare da kashe yan bindiga da dama da suke cikin gidajen da wadanda suka yi yunkurin tserewa

Rundunar sojojin Najeriya ta musamman na Operation Hadarin Daji ta yi nasarar kashe 'yan bindiga da dama sannan ta lalata kayayyakin zirga-zirgansu a wani harin sama da ta kai a dajin Kuyambana da ke Zamfara.

Sojojin sun kai wannan harin ne a jiya Talata 15 ga watan Satumban shekarar 2020 a cikin hare haren saman da suke kai wa a karkashin atisayen Operation Wutan Daji 2 da aka kaddamar domin kawar da 'yan bindiga da sauran miyagu a yankin Arewa maso Yamma.

DUBA WANNAN: Kuma dai: An sake sace jami'in DSS, an nemi N100m a matsayin kudin fansa (Hotuna)

Sojojin sun kai harin ne bayan samun sahihan bayannan sirri da rahotanni tare da amfani da na'urorin leken asiri da suka nuna akwai gidaje da 'yan bindigan ke amfani da su a matsayin mabuya.

Kamar yadda bayanan sirrin suka ce, wasu gine ginen da sojojin suka lalata mallakar hatsabiban shugabannin 'yan bindiga 'Sani Mochoko' da 'Damina' ne da suke amfani da su tare da mayakansu.

Wannan bayannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun hedkwatan tsaro, Manjo Janar John Enenche ya fitar ne a shafin Twitter na rundunar a ranar Laraba, 15 ga watan Satumba.

Jiragen yaki na NAF sun yi ruwan bama-bamai a kan gine ginen inda suka yi wa 'yan bindigan mummunan illa tare da kashe da dama cikinsu.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace tsohon sojan Amurka a Ekiti

Sojojin sun kuma yi amfani da jirage masu saukan ungulu sun karasa 'yan bindigan da suka yi yunkurin tsere wa inda suka rika yi musu dauki dai-dai.

Ga bidiyon yadda aka kai harin a kasa:

A wani labarin daban, kun ji cewa wasu ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun kashe wani Alhaji Mai Yadi sun kuma sace ɗansa, Usman a garin Ƴankara da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayin, Kwamared Younusa Mukhtar ya tabbatar da afkuwar hakan a ranar Talata 15 ga watan Satumba ya ce lamarin ya faru misalin ƙarfe 11 na daren ranar Litinin a gidansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel