Rarara: Bai dace a ba Mawaki gudumuwar kudin waka ba inji Sheikh Yusuf Ya’u

Rarara: Bai dace a ba Mawaki gudumuwar kudin waka ba inji Sheikh Yusuf Ya’u

- Limamin Hadejiya ya yi magana game da kudin da ake aikawa Mawaki Rarara

- Yusuf Abdulrahman Yau ya ce bai dace a turawa Mawakin wata gudumuwa ba

- Babban Limamin ya bayyana wannan ne wajen wani karatu da ya ke yi a Jigawa

Malam Yusuf Abdulrahman Yau, wanda shi ne babban limamin garin Hadejiya, jihar Jigawa, ya yi magana game da kudin da ake tarawa Dauda Kahutu Rarara.

Yusuf Abdulrahman Yau ya ce a halin da ake ciki, bai kamata a bijirowa talaka da maganar bada gudumuwa domin ayi wa shugaban kasa Buhari wata waka ba.

Shehin Malamin ya yi wannan bayani ne a wajen karatun littafin Adabul – Mufrad kamar yadda wani faifen bidiyo da ya shigo hannun Legit.ng Hausa ya bayyana.

Limamin ya ke tsokaci ya na cewa: “Kuma ana wannan yanayin wani ya zo ya na cewa a ba shi N1, 000 zai fitar da wani abu.”

KU KARANTA: Mawaki Rarara ya ba Mai shadda kyautar mota

“Kai ka ji wani rashin hankali, mu na cikin damuwa da bakin ciki, ace za a fitar da wata waka. Ka ji wata masifa fa.” Inji Yusuf Abdulrahman.

"Ba a bar ka da radadi ba, shi kuma wani Naira dubu-dubu ya ke nema domin ya fitar da wata muhimmiyar waka wanda talakawa za su yi dariya.”

Rarara: Bai dace a ba Mawaki gudumuwar kudin waka ba inji Sheikh Yusuf Ya’u
Yusuf Abdulrahman Yau Hoto: Facebook/mal.yusufabdurrahmanyau
Asali: Facebook

Ganin irin halin da ake ciki na tsadar rayuwa da kudin kayan abinci, malamin ya ce, “Yanzu talaka ya daina dariya, idan ka gan shi yanzu sai hawaye ya ke yi.”

Malamin ya ce rashin sanin abin da ya kamata ne a aikawa tauraron kudin rera waka. “Da wannan N1000, ga masallacin unguwarku, ka saye kwan lantarki da ya fi alheri.”

KU KARANTA: Buhari: Malaman addini sun fara fitowa su na kokawa da tsadar rayuwa

Wannan limami ya ce a sa kan fanfo ko fanka a masallaci ya fi alheri a kan a ba Rarara kudin waka.

A karshe Shehin ya ce wakar da za a rangada ba za ta yi wani dadin a zo a gani ba.

Dauda Kahutu Rarara ya bukaci masoyan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari su tattara masa N1000 domin ya rangadawa gwanin na su wata sabuwar waka.

Kafin yanzu mun ji cewa Sheikh Jabir Mai Hula ya yi kira ga al’umma su maida hankali wajen bada sadaka a kan turawa asusun wannan mawakin APC kudi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel