Shugaba Buhari ya bawa shugabannin Afrika shawara a kan maitar son makalewa a mulki

Shugaba Buhari ya bawa shugabannin Afrika shawara a kan maitar son makalewa a mulki

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya roki shugabannin kasashen nahiyar Afrika ta yamma a kan kar su kara wa'adin mulkinsu fiye da abinda kundin tsarin mulkin kasashensu ya ambata.

Buhari ya yi wannan kira ne yayin da yake gabatar da jawabin Najeriya a wurin taron ECOWAS na 57 da aka yi a birnin Niamey na kasar Nijar ranar Litinini.

Kazalika, Buhari ya shawarci abokansa su mutunta kundin tsarin mulkin kasashensu tare da gudanar da zabukan gaskiya.

Hakan na kunshe ne a cikin jawabin shugaba Buhari da kakakinsa, Garba Shehu, ya waallafa a shafukansa na sada zumunta.

"Yana da muhimmanci a wurinmu na shugabannin kasashen da ke zaman mambobi a ECOWAS mu kasance ma su biyayya ga kundin tsarin mulkin kasashenmu, musamman a kan wa'adin mulki. Wannan batu ya dade yana haddasa rigingimu da tashin hankula a yankinmu.

Shugaba Buhari ya bawa shugabannin Afrika shawara a kan maitar son makalewa a mulki
Buhari a wurin taron ECOWAS
Asali: Facebook

"Mu na fuskantar kalubale da dama a wannan yanki na mu kuma bai kamata mu cigaba da haifar da baraka ta hanyar kara tsawon wa'adin mulki ba.

"Ina kira garemu; mu fi karfin zuciyarmu, mu fi karfin rudin maitar son makalewa a mulki fiye da wa'adin da kundin tsarin mulki ya tanadar mana.

KARANTA: Za ka ga bakar zanga-zanga - Kungiyar dalibai ta aikawa Buhari zazzafan sako

KARANTA: Buhari zai kaddamar da shirin tallafawa 'yan kasuwa da N50,000 a kowanne wata

"Ina jinjina ga wadansu daga cikinmu da suka fi karfin zuciyarsu, tabbas tarihi zai cigaba da tunasu a matsayin jarumai a kasashensu da kuma yankin nahiyar Afrika ta yamma.

"Wani muhimmin batu da ke tare da wannan magana shine tabbatar da sashihin zabe na gaskiya, wanda ya yi daidai da zabin jama'a, akwai bukatar yin hakan kamar yadda ake da bukatar mutunta doka da tsari," a cewar wani bangare na jawabin shugaba Buhari.

Yayin taron na ECOWAS, shugabannin kasashen nahiyar Afrika ta yamma sun tattauna akan rikicin kasar Mali da kuma yadda za a tabbatar da cewa kasar ta koma kan mulkin dimokradiyya bayan wata 12.

Kazalika, shugabannin sun tattauna a kan hanyoyin farfado da tattalin arzikin kasashensu da nahiyar Afrika ta yamma bayan sassauta dokar kulle da aka saka sakamakon bullar annobar korona.

Shugaba Buhari ya bawa shugabannin Afrika shawara a kan maitar son makalewa a mulki
Buhari da shugabannin kasashen nahiyar Afrika ta yamma a wurin taron ECOWAS
Asali: Facebook

Shugaba Buhari ya bawa shugabannin Afrika shawara a kan maitar son makalewa a mulki
Shugaba Buhari ya bawa shugabannin Afrika shawara a kan maitar son makalewa a mulki
Asali: Facebook

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel