FG za ta fara cilla tallafi ga 'yan gudun hijira ta jiragen sama

FG za ta fara cilla tallafi ga 'yan gudun hijira ta jiragen sama

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da shirinta na fara bai wa kauyukan arewa maso gabas agaji ta hanyar cilla wa 'yan gudun hijira abinci ta sama.

Ministan kula da walwala da jin kan 'yan kasa, Sadiya Farouk, ta shaida wa 'yan jarida a Maiduguri.

A ranar Lahadi ta sanar da cewa za a fara yin amfani da jiragen sojin saman Najeriya domin wurga kayayyakin tallafi kamar su bargo da abinci.

Ta sanar da cewa akwai manyan matsalolin da suke fuskanta na kai wa ga jama'ar da ke cikin kauyuka. Hakan yasa tace za su fara Villa kayan ta jiragen sama ga kauyukan da motoci basu iya zuwa.

Yankin arewa maso gabas na Najeriya na daga cikin yankunan da ta'addanci da rashin kwanciyar hankali ya addaba a Najeriya.

Mayakan ta'addancin na Boko Haram sun kasance suna cin karensu babu babbaka a yankin tun a 2009.

Hakan ya kawo mutuwar jama'a masu yawa tare da sanya wasu suka bar gidajensu domin neman mafaka a sassa daban-daban na kasar nan har da ketare.

FG za ta fara cilla tallafi ga 'yan gudun hijira ta jiragen sama
FG za ta fara cilla tallafi ga 'yan gudun hijira ta jiragen sama. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Maigadi ya rasu bayan ya sha giya sannan ya kwanta da takunkumin fuska

A wani labari na daban, a kalla mutum hudu cikin 'yan gudun hijira mayakan Boko haram suka yi awon gaba da su a yayin da suke gonakinsu a kusa da Maiduguri a ranar Talata, wasu majiyoyi suka tabbatar.

An gano cewa, mayakan Boko Haram sun kutsa Dalwa da ke kusa da yankin Molai a Maiduguri da ke jihar Borno.

Sun kai wa manoman hari tare da yin awon gaba da hudu daga ciki. Ganau ba jiyau ba da suka bada labari, sun ce mayakan ta'addancin sun kai harin a kan babura ga manoman da basu da mataimaka.

Mallam Babagana, wanda ya sha da kyar daga harin 'yan ta'addan ya ce a kan idonsa aka kwashe mutane hudun.

Da kanshi ya bayyana wa iyalan wadanda lamarin ya shafa. Hakan kuwa ya janyo tashin hankali a sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi.

"A yau, daya ga watan Satumban 2020, wurin karfe 4:20 na yammaci mayakan Boko Haram suka kutsa gonakin 'yan gudun hijira da ke Dalwa a Molai suka yi awon gaba da mutane hudu," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel