Hotuna da bidiyon ranar daurin auren Hanan Buhari da Turad Sha'aban
A ranar Juma'a, 4 ga watan Satumban 2020 aka daura auren Aisha Hanan Buhari, autar shugaban kasar Najeriya, da Muhammad Turad Sha'aban, mai bai wa ministan ayyuka shawara na musamman, Babatunde Fashola.
An yi gagarumin daurin auren a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke Aso Villa a Abuja.
Sakamakon annobar korona da ta zama ruwan dare, tun a katin gayyatar an bayyana cewa ba za a yi bikin cike da taro ba domin biyayya ga dokokin hukumar dakile yaduwar cututtuka.
Cike da farin ciki tare da mika godiya ga masoya, 'yan uwa da abokan arziki, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta wallafa bidiyon yadda aka daura auren da kuma hotunan shagalin bikin.
Kamar yadda ta wallafa a shafinta na Instagram, ta ce "A yau babbar rana ce ta farin ciki ga iyalaina a yayin da muka shaida auren diyata Aisha Hanan Buhari da Muhammad Turad Sani Sha'aban.
"Ina matukar farin ciki da sakonnin fatan alheri da kuma goyon baya daga iyalaina, abokai da masoya.
"Bari in yi amfani da wannan damar wurin mika sakon godiya ga wadanda suka samu damar halarta da wadandan basu samu dama ba.
"Sakamakon fahimtar wannan lokaci na tsananin annobar duniya da muka yi da kuma bukatar kiyaye shawarwarin masana kiwon lafiyarmu na karanta taro.
"Muna godiya a kan addu'o'inku ga ma'auratan a yayin da suka shiga sabuwar rayuwar aure."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng