Makasan maza: Yadda matasa suka bi 'yan bindiga, suka kashe 1 tare da kwato shanunsu

Makasan maza: Yadda matasa suka bi 'yan bindiga, suka kashe 1 tare da kwato shanunsu

Jama'a mazauna kauyen Sabon Garin Nasarawa da ke karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina sun zama jajirtattu, jaridar Katsina Post ta wallafa.

Jama'ar sun tattara duk wata jarumtarsu tare da yin gaba-gaba da wasu 'yan bindigar daji wadanda suka kai musu hari a sa'o'in farko na ranar Talata da ta gabata.

Kamar yadda rahotanni daga Katsina Post suka bayyana, 'yan bindigar masu tarin yawa a kan babura sun tsinkayi kauyen wurin karfe 12:30 na ranar Talata.

Sun yi awon gaba da dabbobinsu, kayan abinci da abubuwa masu muhimmanci na jama'ar kauyen.

Amma kuma bayan da 'yan bindigar suka sakankance cewa sun yi nasara, matasan sun yi jarumta inda suka zagaye gonaki tare da dazuzzukan da ke kusa.

Rahotanni sun bayyana cewa, matasan sun yi nasarar kashe daya daga cikin 'yan bindigar tare da kwato dabbobinsu da suka sace.

Amma kuma, a wannan karon, 'yan bindigar sun kashe daya daga cikin mazauna kauyen tare da raunata wani, wanda a halin yanzu yake gadon asbiti inda ake kula da shi.

Makasan maza: Yadda matasa suka bi 'yan bindiga, suka kashe 1 tare da kwato shanunsu
Makasan maza: Yadda matasa suka bi 'yan bindiga, suka kashe 1 tare da kwato shanunsu. Hoto daga Katsina Daily Post
Asali: Twitter

KU KAARANTA: 'Yan sa kai sun fatattaki masu garkuwa da mutane, sun kashe 3 a take

A wani labari na daban, dakarun rundunar Operation Sahel Sanity sun kashe 'yan bindiga biyu, sun damke 12 daga ciki tare da ceto wasu jama'a masu yawa da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Zamfara a makon da ya gabata.

Wannan na kunshe ne a wata takardar da mukaddashin daraktan yada labarai na hukumar tsaro, Birgediya Janar Benard Onyeuko ya fitar a ranar Litinin.

Onyeuko ya ce, "A ranar 28 ga watan Augustan 2020, dakarun sojin Najeriya da ke Maru sun kai wa wasu da ake zargin 'yan bindiga samame yayin da suke kokarin shiga kauye Gobirawa.

"Cike da kwarewar dakarun tare da taimakon 'yan sa kai, sun hana 'yan bindigar shiga kauyen.

"A yayin samamen, dakarun sun yi musayar wuta da 'yan bindigar inda suka kashe biyu daga ciki, amma wasu sun tsere da miyagun raunika. An ga jini a kasa wanda ya bayyana hanyar da suka bi."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel