Zamfara za ta fara yankewa masu tukin ganganci hukuncin kisa bayan mutuwar wasu magoya bayan gwamnan su 15
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya ce gwamnatinsa za ta kafa hukuncin kisa ga direbobi masu tukin ganganci a jihar.
Ci gaban na zuwa ne bayan mutuwar magoya bayansa 15 a wani hatsarin hanya bayan sun yi masa maraba da zuwa karamar hukumar Tsafe.
Hatsarin ya afku ne lokacin da wata babbar mota ta kwace sannan ta je ta daki ayarin motoci hudu na magoya bayan Matawalle a hanyar Gusau-Funtua da ke Tsafe.
A cikin wani jawabi a ranar Asabar, Yusuf Idris, daraktan labarai da waye kan jama’a na gwamnan, ya ce za a samar da hukuncin kisa a matsayin matakin hukunta direbobi masu tukin ganganci.
Idris ya ce gwamnan ya yanke wannan hukunci ne lokacin da ya jagoranci mambobin majalisarsa da hukumar kamfanin BUA a wani ziyarar jaje da suka kai fadar Ibrahim Bello, sarkin Gusau, kan mutuwar mutum 15.
Ya ce sabuwar dokar za ta tabbatar da ganin cewa an tilasta wadannan direbobi biyan diya a kan duk wani raid a aka rasa.
Matawalle ya sanar da bayar da gudunmawar naira miliyan 2 ga kowani iyali na mamatan wadanda ked a mata, naira miliyan 1.5 ga iyalan mamatan da basu da mata.

Asali: UGC
Ya ce za a saka magajin kowani mamaci a cikin jerin wadanda jiha za ta dunga biyan alawus din N50,000 duk wata har zuwa karshen wa’adin mulkinsa.
Gwamnan ya kara da cewar gwamnatinsa za ta samar da iyakar gudun da motoci za su dunga yi a manyan titian, ma’aunin kayayyaki kan manyan motoci.
Za kuma a dunga yi wa direbobin gwajin kwaya domin hana tukin ganganci, wanda ke yawan haifar da mace-macen rayuka.
Matawalle ya ce sabuwar dokar zai tabbatar da ganin cewa direbobi sun dandana kudarsu na daukar rayuwan jama’a a jihar.
Ya bukaci shugabannin kamfanin BUA da su ja wa direbobinsu kunne a kan adadin gudu da aka amincewa masu tuki su yi.
KU KARANTA KUMA: Yadda ‘yan iska suka yi wa wata matashiya fyade sannan suka kashe ta a Ibadan
A nashi jawabin, Aminu Suleiman, Shugaban tawagar kamfanin BUA, ya ce tawagar ta zo yin ta’aziyya ne ga gwamnati, masarautar Gusau, mutanen jiha da kuma iyalan wadanda aka kashe sakamakon wani hatsari da ya cika da direban kamfanin.
Sarkin ya yaba ma Matawalle da kamfanin BUA kan kulawarsu, inda y ace dukkan mai rai mamaci ne.
Ya kara da cewar za a yi amfani da gudunmawar da aka bayar sosai ta yadda ya dace.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng