Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun kashe mutane 2 tare da awon gaba da dan sanda

Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun kashe mutane 2 tare da awon gaba da dan sanda

- Yan bindiga sun afkawa garuruwan Mararraban Rido da Juji da ke a karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna, inda suka kashe mutane biyu

- Har ila yau, 'yan bindigar sun yi awon gaba da dan sanda maras lafiya, yarinya mai shekaru 14, jami'in NSCDC da kuma mai gadi

- Yan bindigar sun fara kai harin ne a gidan shugaban kungiyar CAN reshen karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Rev. Elisha Abu

A ranar Juma'a wasu 'yan bindiga suka afkawa garuruwan Mararraban Rido da Juji da ke a karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna, inda suka kashe mutane biyu.

Yan bindigar sun kashe mutane biyu a Juji, ya yin da suka afkawa garin Maraban Rido, inda suka yi awon gaba da mutane hudu ciki har da dan sanda, maras lafiya.

An shaidawa manema labarai cewa daga cikin wadanda aka sace a harin da suka kai, har da yarinya mai shekaru 14, jami'in NSCDC da kuma mai gadi.

Wata majiya ta shaida cewa 'yan bindigar sun fara kai harin ne a gidan shugaban kungiyar CAN reshen karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Rev. Elisha Abu kafin shiga wasu gidajen.

KARANTA WANNAN: Buhari ya yi magana kan fadowar jirgi mai ungulu a jihar Lagos

Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun kashe mutane 2 tare da awon gaba da dan sanda
Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun kashe mutane 2 tare da awon gaba da dan sanda
Asali: Depositphotos

Elisha Abu ya tabbatar da harin, yana mai cewa 'yan bindigar sun fara kai farmaki a gidansa da misalin karfe 11:57 na daren ranar Alhamis, inda suka yi kokarin shiga gidan amma suka kasa.

Ya bayyana cewa bayan sun bar kofar gidansa ne sai suka shiga gidajen da ke makwaftaka da shi, inda suka tafi da "wani dan sanda maras lafiya, wanda ya zo daga wata jiha.

"Sun kuma tafi da jami'in Civil Defence, yarinya mai shekaru 14 da kuma wani mai gadi. Duk sun yi garkuwa da shi."

A garin Juji da ke makwaftaka da Maraban Rido kuwa, nan ma 'yan bindigar sun yi harbe harbe inda suka kashe mutane biyu.

Wadanda aka kashen, 'yan wani gari ne da suka zo kawo dauki. Yan bindigar sun fara kaddamar da harin nasu da misalin karfe 11 na dare har zuwa shigar ranar Juma'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel