Jihar Filato ta zama filin dagar yaki da annobar COVID-19 inji PTF

Jihar Filato ta zama filin dagar yaki da annobar COVID-19 inji PTF

Gwamnatin tarayya ta fito ta bayyana inda aka kwana wajen yaki da annobar COVID-19. Coronavirus ta jawo tabarbarewar abubuwa a Najeriya da Duniya.

Daga cikin sanarwar da gwamnati ta bada a jiya shi ne, an dage ranar dawo da tashin jiragen sama daga gobe 29 ga watan Agusta har sai zuwa ranar 5 ga watan Satumba.

Shugaban hukumar NCAA na kasa, Musa Shuaibu Nuhu, ya bada wannan sanarwa a Abuja.

Bayan haka kwamitin PTF ta ce cutar ta yi kamari a Jihar Filato. A halin yanzu an yi kwanaki biyu a jere Filato ta na zama kan gaba a jihohin da ake samun bullar Coronavirus.

Shugaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da annobar COVID-19, Boss Mustapha ya bayyana cewa Filato ta sha gaban kowace jiha a yau, ta zama abin damuwa.

A baya jihohi irinsu Legas, Kano, Ogun da Oyo ne cutar ta yi kamari. A ‘yan kwanakin nan, alkaluma sun tabbatar babu inda ake samun bullar COVID-19 irin jihar Filato.

KU KARANTA: Mutum 1, 000 da su ka kamu da Coronavirus sun mutu a Najeriya

Jihar Filato ta zama babbar filin dagar yaki da annobar COVID-19 inji PTF
SGF Boss Mustapha, shi ne shugaban PTF
Asali: Twitter

Boss Mustapha ya ce ko da Legas ta zarce intaharta, bai kamata a saki jiki ba. Mista Mustapha ya yi wannan jawabi ne a madadin PTF a lokacin da ya zanta da ‘yan jarida a jiya.

Ya ce: “Yayin da mu ke shiga makon karshe na takunkumin da aka tsawaita, da la’akari da raguwar wadanda su ke mutuwa da karancin masu kamuwa da cutar, PTF za ta ja hankalin mutane game da canjin da aka samu a yaduwar cutar.”

“Za mu tuna cewa Legas, Kano, da Ogun ne da inda cutar ta yi kamari, daga nan ta koma Oyo a wani lokaci, yanzu abin ya koma Filato.” inji Mustapha.

Sakataren gwamnatin tarayya ya ce kamar yadda kwamishinan lafiya na Legas, Akin Abayomi, ya fada, ana samun sa’ida a jihar, amma hakan ba ya nufin an kawo karshen annobar.

“Burinmu shi ne mu yi wa dinbin mutane gwaji a fadin kasar nan.” Inji shugaban kwamitin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel