'Yan gudun hijira na shiga kungiyar Boko Haram - Gwamna Zulum ya koka

'Yan gudun hijira na shiga kungiyar Boko Haram - Gwamna Zulum ya koka

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya koka kan cewa kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram na ci gaba da daukar sabbin mutane, musamman daga sasanin ‘yan gudun hijira.

A cewar gwamnan: “gaskiya, kungiyar Boko Haram na aiki kan mutane domin su shiga cikinta. Hakan abun tsoro ne.

"Idan ‘yan gudun hijira da ke zama a sansanoni basu samu abunda suke nema ba, musamman damar komawa garuruwansu daban daban da komawa gonaki, hakan na iya tursasa su shiga kungiyar Boko Haram."

Zulum ya yi magana ne a wata hira da sashin Hausa na BBC, wanda manema labarai suka bibiya a Kaduna.

Ya yi bayanin cewa ‘yan gudun hijira sun gaji da zama a sansanonin saboda basu samun abubuwan da suke so.

“Yana da matukar muhimmanci cewa su koma garuruwansu mabanbanta saboda babu gwamnatin da za ta iya i gaba da ciyar dasu,” in ji shi.

Ya ce zuwa yanzu, gwamnatinsa ta yi nasarar mayar da ‘yan gudun hijira zuwa Mafa da Kukawa, yayinda take kokarin dawo da mutane Kawuri.

Ya nuna karfin gwiwar cewa sojoji za su kara kaimi da kokari da kuma ganin an mayar da mutane Baga, Marte, Malam Fatori da Guzamala.

Ya ce: "Amma muna fatan sojoji za su kara kaimi wajen ganin an mayar da al'ummar Baga da Marte da Malam Fatori da Guzamala".

Zulum ya bayyana cewa akwai ci gaba a lamarin tsaro a jihar Borno, amma cewa har yanzu akwai hatsari domin akwai burbudin ‘yan Boko Haram a mabuyarsu.

Sai dai kuma, Zulum ya lura cewa kakkabe Boko Haram daga Sambisa na bukatar tallafi daga kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.

'Yan gudun hijira na shiga kungiyar Boko Haram - Gwamna Zulum ya koka
'Yan gudun hijira na shiga kungiyar Boko Haram - Gwamna Zulum ya koka
Asali: Facebook

Ya ce: "'Yan kungiyar na fakewa a tafkin Chadi da kuma dajin Sambisa. Kuma idan har ba a bi su har ciki ba an kore su ba to fa akwai matsala. Korar su daga hedikwatarsu ita ce hanya guda daya ta kawo karshen Boko Haram."

Dangane da tambayar da aka yi wa Gwamna Zulum ko akwai wasu wurare da kungiyar Boko Haram ke rike da su a jihar ta Borno? Sai gwamna ya ce "gaskiya fisabilillahi babu wani yanki da ke hannun kungiyar Boko Haram, sai akwai yankunan da babu jama'a a cikinsu. Abin da nake nufi shi ne har yanzu jama'a ba su koma garuruwansu ba."

Ya kara da cewa "wallahi kafin zuwan Shugaba Buhari yanayin tsaro a jihar Borno ya yi muni kwarai saboda a lokacin kananan hukumomi 20 ne a karkashin Boko Haram amma yanzu ba haka ba ne."

KU KARANTA KUMA: Zaben shugaban kasa na 2023: Kwanan nan za mu shayar da ‘yan Najeriya mamaki - APC

Gwamna ya ce "hanya daya ta kawo karshen Boko Haram ita ce tabbatar da alaka mai kyau tsakanin sojoji da farar hula."

Ya kara da cewa "na sha magana cewa duk inda ka je za ka ga sojoji da 'yan banga tare. Amma abin da nake cewa shi ne sojoji su bai wa farar hula kariya domin samun damar komawa gidajensu su yi noma."

Farfesa Zulum ya kuma ce tabbas sojoji na iya bakin kokarinsu amma abin da ya "dame mu shi ne yaushe ne wannan yaki na Boko Haram zai kare."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel