Dole mu mayar da kasar Mali cikin hayyacinta - Sakon Buhari ga ECOWAS

Dole mu mayar da kasar Mali cikin hayyacinta - Sakon Buhari ga ECOWAS

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi kira ga sauran shugabannin nahiyar Afrika da su tashi haikan domin ganin kasar Mali ta koma cikin hayyacinta.

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne yayin da ya ke gabatar da jawabi a wurin taron shugabanni ECOWAS da aka yi ranar Alhamis domin daukan matakan warware rikicin kasar Mali.

Tuni ECOWAS ta sakawa kasar Mali takunkumi tare da bawa sauran kasashen ECOWAS da ke makwabtaka da Mali umarnin su rufe iyakokinsu da kasar har sai sun koma turbar dimokradiyya.

Yayin taron, shugaba Buhari ya bayyana cewa juyin mulkin da sojoji su ka yi a kasar Mali zai shafi batun tsaro da zaman lafiya a yammacin Afrika.

"Abinda ya faru a kasar Mali ba kankanin koma baya ba ne da zai iya shafar zaman lafiya da tsaro a kasashen nahiyar Afrika.

"Lokaci ya yi da ya kamata haramtacciyar gwamnatin kasar Mali ta yi abinda ya dace, ta bi kundin tsarin mulki tare da tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar," a cewar Buhari.

Dole mu mayar da kasar Mali cikin hayyacinta - Sakon Buhari ga ECOWAS
Dole mu mayar da kasar Mali cikin hayyacinta - Sakon Buhari ga ECOWAS
Asali: Twitter

Sannan ya cigaba da cewa; "Najeriya ta goyi bayan shugaban ECOWAS, shugaba Mahamadou Issoufou, a kan daukan tsauraran matakai da zasu gaggauta warware matsalolin da kasar Mali ta shiga.

DUBA WANNAN: Annobar korona: Jerin jihohi 16 da suka samu tallafin N1.6bn daga bankin duniya

"Zaman lafiyar kasar Mali yana da matukar muhimmanci ga yankin Afrika ta yamma. Dole mu hada karfinmu wuri guda a matsayin ECOWAS, AU, UN, da sauran ma su ruwa da tsaki har sai mun tabbatar al'amura a kasar Mali sun daidaita, an koma tsarin gwamnati na jama'a."

Buhari ya gana tare da sauran shuwagabannin kungiyar kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) a ranar Alhamis, 20 ga watan Agusta, 2020.

Ganawar tana gudana ne ta kafar yanar gizo, kamar yadda shafin fadar shugaban kasa ta wallafa a shafinta na Twitter.

Shuwagabannin ECOWAS, sun yi wannan ganawar ne a ci gaba da neman hanyoyin daidaita rikicin siyasa da ya barke a kasar Mali, wanda ya kai ga sojoji sunyi juyin mulki a ranar Talata, 18 ga watan Agusta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel