Daukan ma'aikata 774,000: 'Yan majalisa sun raina guraben mutane 30 da aka bawa kowannensu

Daukan ma'aikata 774,000: 'Yan majalisa sun raina guraben mutane 30 da aka bawa kowannensu

- Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai ya raina guraben mutane 30 da aka bawa kowannensu a yayinda gwamnatin tarayya ke shirin daukar ma'aikata 774,000

- An ba kowani dan majalisa hurumin kawo mutum 30 cikin 1000 da za a dauka a kowace karamar hukuma

- Shugaban marasa rinjaye a majalisar ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta duba shirin don tabbatar da cewa talakawa sun amfana

Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, ya ce bai wa 'yan majalisar gurabe talatin- talatin na daga cikin gurabe 1,000 a duk karamar hukuma bai dace ba kuma babu adalci.

Shugaban marasa rinjaye kuma dan majalisa daga jihar Delta karkashin jam'iyyar PDP, Ndudi Elumelu ,ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a kan ayyukan.

Ya ce a matsayin wakilai na jama'a, bai kamata a ba su gurabe 30 ba a mazabunsu.

Elumelu ya ce suna bukatar adalci a wurin sharuddan bada guraben aikin.

Ya zargi sharuddan da bai wa 'yan jam'iyyar APC fifiko kuma hakan illa ne ga 'yan Najeriya.

Daukan ma'aikata 774,000: 'Yan majalisa sun raina guraben mutane 30 da aka bawa kowannensu
Daukan ma'aikata 774,000: 'Yan majalisa sun raina guraben mutane 30 da aka bawa kowannensu Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Ya tabbatar da cewa guraben ayyukan 774,000 da aka bada na talakawa ne kuma ta wannan hanyar ne kadai za a iya tallafawa talakawan.

Kamar yadda yace: "Guraben mutum 30 ga dan majalisa a kowacce karamar hukuma bai dace ba kuma 'yan Najeriya ba za su yarda da hakan ba.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: 'Yan sanda sun ceto matan dan majalisar da 'yan bindiga suka kashe

"A matsayinmu na wakilan jama'a, mun fi kusanci da su kuma muna tattaunawa da su kai tsaye ba tare da banbancin siyasa ko addinai ba.

"Dukkan 'yan Najeriya da ke mazabunmu suna da hakki a kanmu ba tare da duban banbancin siyasa ba. A don haka dole ne a sake duba lamarin.

"Hakazalika, wadanne sharudda ne aka duba har aka ba mu gurabe talatin- talatin?

"Ta yaya za mu tabbatar da cewa shirin ya amfani 'yan Najeriya?"

Ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta duba shirin don tabbatar da cewa talakawa sun amfana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel