'Yan sanda sun kama tsohon da ya sace yarinya yana bada haya don lalata da ita

'Yan sanda sun kama tsohon da ya sace yarinya yana bada haya don lalata da ita

- Rundunar 'yan sandan Taraba na bincike a kan wani tsoho mai shekaru 67 da kuma wasu mutum biyu a kan zargin su da ake da killace wata yarinya

- An tattaro cewa sun tsare yarinyar mai shekaru 11 tare da yi mata fyade akai-akai

- Tsohon na amsar kudi daga hannun wani mutum da ke zuwa ya dauki karamar yarinyar a mota ya tafi da ita don lalata

Rundunar 'yan sandan jihar Taraba ta tabbatar da cewa tana bincike a kan wani tsoho mai shekaru 67, da kuma wasu mutum biyu a kan zargin su da ake da killace wata yarinya mai shekaru 11 suna yi mata fyade.

Ana zargin mutum ukun da yin lalata da yarinyar na dogon lokaci inda suke karba-karba da ita a babban birnin jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, ya ce tsohon ya rika amsar kudi daga hannun wani mutum da ke zuwa ya dauki karamar yarinyar a mota ya tafi da ita don lalata.

KU KARANTA KUMA: An birne tsohuwar kwamishinar da ta rasu a jihar Katsina

'Yan sanda sun kama tsohon da ya sace yarinya yana bada haya don lalata da ita
'Yan sanda sun kama tsohon da ya sace yarinya yana bada haya don lalata da ita Hoto: The Guardian
Asali: UGC

"A yanzu akwai wani wanda alama ke nuna cewa yana zuwa wurin dattijon yana daukar yarinyar a mota yana kaita wani wuri inda yake lalata da ita," DSP David Misal yace.

A halin yanzu an fara bin sahun mai motar don kama shi.

Dan sandan ya ce tsohon he ya fara tsintar karamar yarinyar a tashar motar birnin Jalingo, kuma ya ajiyeta a hannunsa na tsawon watanni uku.

"Tsohon yana aikin gadi a wani gidan mai inda ya shigar da ita yake lalata da ita na kusan wata uku. Amma ba shi kadai bane."

David Misal ya ce tsohon ya kara da gayyato abokansa biyu wadanda suka rika zuwa suna yi mata fyade kafin asiri ya tonu.

KU KARANTA KUMA: Zanga-zangar yi wa Annabi batanci: An kashe mutum 3 a kasar Indiya

Ya ce a halin yanzu sun mayar da hankali wurin bincike don samun damar gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.

Rundunar 'yan sandan ta tabbatar sa cewa tuni ta tura karamar yarinyar sashenta na musamman don samun kulawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel