SERAP ta na so Gwamnati ta fito da Shariff da sauran masu laifin batanci a Najeriya

SERAP ta na so Gwamnati ta fito da Shariff da sauran masu laifin batanci a Najeriya

Kungiyar SERAP ta yi tir da hukuncin da wani Alkalin babban kotun shari’a ya yanke na kisan kai a kan Yahaya Sharif-Aminu wanda ya zagi Manzon Allah a Kano.

A farkon makon nan ne Alkali mai shari’a Aliyu Kani ya samu yaro mai shekara 22 da laifin yin batanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW.

Kungiyar ta SERAP ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi fatali da hukuncin da aka yi wa wannan matashi, ta ce Alkalin kotun shari’ar ya yi wa dokar kasa karon-tsaye.

A cewar SERAP, an tauyewa wannan Mawaki watau Yahaya Sharif-Aminu hakkinsa na magana a matsayinsa na ‘dan kasa da wannan hukuci da kotun shari’a ta yanke.

A dalilin wannan ne kungiyar ta fito ta na neman gwamnati ta sa baki, a saki Sharif-Aminu. SERAP ta bayyana wannan ne a shafinta na Twitter a ranar 11 ga wata Agusta, 2020.

Wannan kungiya ta ce hukuncin ya nuna yadda ake azabtar da talaka a Najeriya da rigar dokokin batanci. SERAP ta ce dokar ta na aiki ne kurum a kan talaka maras gata.

KU KARANTA: Abin da addini ya ce a kan masu zagin Annabi - Sanusi II

SERAP ta na so Gwamnati ta fito da Shariff da sauran masu laifin batanci a Najeriya
Yahaya Sheriff-Aminu
Asali: Facebook

Bayan haka kungiyar SERAP ta bukaci gwamnatin tarayya ta soke duk wasu dokokin batanci da su ka ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da dokokin Duniya.

“Hukumomi su yi watsi da dokokin batanci, su daidaitasu da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da dokokin kasashen waje na kare hakkin Bil Adama wanda Najeriya ta yi amanna da su.”

“Bai kamata a rika kawo laifin batanci a kan mutane don kurum sun yi amfani da damarsu ba, daga ciki har da damar magana.” Inji SERAP.

An kuma samu lauyoyi da masu kare hakkin mutane a Najeriya da su ka fito su na sukar wannan hukunci da masu kishin addinin Musulunci su ka yi maraba da shi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel