Harin Zulum: An bai wa Buhari shawarar mayar da shugabannin tsaro arewa maso gabas

Harin Zulum: An bai wa Buhari shawarar mayar da shugabannin tsaro arewa maso gabas

- Wata kungiyar matasa ta bukacci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya mayar da shugabannin tsaro yankin arewa maso gabas

- Kungiyar ta yi wannan kira ne sakamakon harin da aka kai wa gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum a kwanakin baya

- Kungiyar ta ce rashin hana afkuwar harin ya tozarta Najeriya a idon duniya

Wata kungiyar matasa mai suna YouthAid Nigeria, ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta mayar da ofisoshin manyan kwamandojin tsaro yankin arewa maso gabas.

Kungiyar ta gabatar da wannan bukata tata gaban shugaban kasar ne a kan harin da aka kai wa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin INEC, ta dawo da jam'iyyun siyasa 23, za a dangana kotun koli

Harin Zulum: An bai wa Buhari shawarar mayar da shugabannin tsaro arewa maso gabas
Harin Zulum: An bai wa Buhari shawarar mayar da shugabannin tsaro arewa maso gabas Hoto: Pulse
Asali: UGC

Daraktan kungiyar, Smart Edwards, a wata takarda da ya fitar ranar Litinin, ya ce rashin iya dakile harin daga garesu ya janyo wa Najeriya abun kunya.

"Muna kira ga shugaba Buhari da ya gaggauta bai wa kwamandojin damar komawa yankin arewa maso gabas," yace.

A wani labarin kuma, kungiyar gwamnonin arewa maso gabas sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tura 'yan sanda don yakar Boko Haram a yankin.

Kungiyar ta sanar da hakan ne a wata takarda da ta fitar bayan taronta karo na biyu da tayi don tattaunawa a kan kalubalen da yankin ke fuskanta.

Takardar ta samu saka hannun shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum.

Ta jinjinawa kokarin gwamnatin tarayya wurin yaki da ta'addancin, amma tayi kira ga dakarun soji da su tsananta tsaro wurin tabbatar da cewa manoma a yankin za su iya komawa gonakinsu.

KU KARANTA KUMA: Muna roƙon 'yan Najeriya su ƙara haƙuri kan matsalar rashin tsaro - Buhari

Ta yi kira ga ma'aikatar ruwa ta tarayya da ta mayar da hankali wurin cike tafkin Chadi tare da karfafa sauran rafukan da ke yankin.

Takardar ta ce, gwamnonin shida sun dauka alwashin aiki tare don tabbatar da hadin kai, ci gaba da habakar yankin ballantana a fannin hako man fetur, noma da kuma masana'antu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel