Abubuwa 12 da ya kamata ku sani game da marigayi Sanata Buruji Kashamu
A ranar Asabar, 8 ga watan Agusta ne aka sanar da mutuwar sanata mai wakiltan Ogun ta gabas, Buruji Kashamu, bayan ya yi fama da cutar korona.
Sanata Murray Bruce ne ya sanar da mutuwar sanatan a shafinsa na Twitter.
Ga wasu ‘yan abubuwa da baku sani ba game da marigayi dan siyasan.
1. An haifi Kashamu a jihar Ogun, a ranar 19 ga watan Mayu 1958.
2. Ya fara karatunsa a makarantar firamare na Ansarudeen, Ijebu Igbo sannan ya bar makarantar a 1972 inda ya kammala karatunsa na firamare a St. John Modern School, Lagos.
3. Kashamu ya kuma halarci makarantar yamma a kwalejin Igbobi yayinda yake aiki a matsayin jami’in lasisi.
4. Daga bisani ya je Landan inda ya yi darusa a fannin kasuwanci a Kwalejin Pitman, Landan.
5. An karrama Kashamu da digiri na uku a jami’ar Cambridge Graduate University, da ke Massachusetts, a wani kasaitaccen taro da aka shirya a Lagas.
6. Ya kasance jigo a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ogun.
7. Ya tsaya takara kujerar sanatan Ogun ta gabas sannan ya kayar da abokin adawarsa da kuri’u 99,540.
8. An nada dan siyasan a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na PDP a yankin kudu maso yammacin Najeriya.
9. A 2018, an dakatar dashi daga jam’iyyar Peoples Democratic Party, hukuncin da wata kotun Abuja ta soke a watan Oktoba 2018.
KU KARANTA KUMA: Sarkin Kano da Sarkin Bichi sun kai ziyarar mubaya'a ga sarkin Gwandu
10. Ya kasance dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Ogun kuma ya sha kaye a hannun Dapo Abiodun na jam’iyyar APC.
11. A 1998, an kama Kashamu a kasar Amurka kan lamari da ya shafi miyagun kwayoyi bayan ya yi kokarin shiga kasar da zunzurutun kudi har $230,000.
12. An wanke shi sannan aka sake shi a 2003.
A gefe guda, Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya aika sakon ta'azziyarsa ga gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, bisa rasuwar Sanata Buruji Kashamu.
A wasikar da ya aike ranar Asabar, 8 ga Agusta, Obasanjo ya siffanta mutuwar Kashamu a matsayin babban abin rashi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng