Yadda matashi dan shekara 22 ya nitse cikin kogi a Kano

Yadda matashi dan shekara 22 ya nitse cikin kogi a Kano

Wani matashi dan shekara 22 mai suna Yusuf Abdullahi, ya nitse yayinda yake wanka a cikin wani kogi a Danhassan, a karamar hukumar Kura da ke jihar Kano.

Malam Saidu Mohammed, jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano ne ya sanar da hakan, a cikin wani jawabi zuwa ga manema labarai a Kano a ranar Lahadi, 2 ga watan Agusta.

Ya ce: “Mun samu wani kira mai cike da damuwa a ranar Lahadi daga wajen wani Malam Sadi Ibrahim, da misalin karfe 03:31 na rana, cewa an tsinci gawar Abdullahi yana yawo a kogin.

“Muna samun labarin, sai muka aika tawagar ceto zuwa wajen da misalin karfe 03:42 na rana.

Yadda matashi dan shekara 22 ya nitse cikin kogi a Kano
Yadda matashi dan shekara 22 ya nitse cikin kogi a Kano Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

“An fito dashi sannan aka mika shi ga hakimin kauyen Garin Kaya, Alhaji Aminu."

Ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike a kan abunda ya haddasa mutuwar nasa, jaridar Daily Drust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Bikin sallah: Sanata Shehu Sani ya wallafa hotunan kyawawan ‘ya’yansa

A wani labari na daban, babban sakataren hukumar kula da al'amuran gaggawa na jihar Bauchi, SEMA, Shehu Ningi, ya ce kusan mutum 15 suka rasu sakamakon nitsewar da kwale-kwale tayi a kauyen Gwaskaram da ke karamar hukumar Bauchi ta jihar.

Ningi ya tabbatar da aukuwar lamarin ne a wata tattaunawa da yayi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Bauchi.

Ya ce kwale-kwalen na dauke da fasinjoji daga kauyen Gwaskaram inda suka nufi kauyen Yola Doka don cin kasuwa.

Ningi ya ce lamarin ya faru ne a cikin kwanakin karshen mako a rafin Gwaskaram da ke karamar hukumar Bauchi ta jihar.

Ya ce an tabbatar da mutuwar mutum 15 yayin da aka ceto mutum uku duk da dai har yanzu ana ci gaba da neman sauran.

Babban sakataren SEMA ya tabbatar cewa ana ci gaba da neman sauran gawawwakin a cikin rafin, jaridar Daily Nigerian ta tabbatar.

Ningi ya ce kwale-kwalen ta nitse ne sakamakon cika jama'a da aka yi da kuma rashin gyara. Wani rami ne gareta inda ruwa ya dinga shiga har ta nitse.

Ya ce kwale-kwalen na dauke da mutane 21 ne kuma ko daga gani an san ta yi musu kadan.

Dagacin kauyen Gwaskaram, Abdullahi Maikano, ya sanar da NAN a tattaunawar waya, cewa kwale-kwalen na dauke da sama da mutum 20 lokacin da ta nitse.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel