Idan kun isa ku ce kule ku gani a kan yaki da rashawa - Buhari ya yi wa PDP martani
- Gwamnatin tarayya ta ce babu abunda ya sami yaki da cin hanci da rashawa da take yi, cewa yana nan daram
- Ta kalubalanci duk wanda yake ganin ba gaskiya bane yakin da take yi da ya jarraba ya gani
- Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya yi wannan tsokacin a yau Talata, 28 ga watan Yuli, a Abuja
- Ya kuma yi watsi da kiran da babbar jam'iyyar adawa ta PDP ke yi na neman Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi murabus
A ranar Talata, gwamnatin tarayya ta ce babu abunda ya sami yaki da cin hanci da rashawa da take yi, cewa yana nan daram.
Daga nan gwamnatin tarayyar ta ce duk wanda yake ganin ba gaskiya bane hakan, musamman ‘yan jam’iyyar adawa, toh su gwada su gani sannan su shirya karbar hukunci.
Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a birnin Abuja, jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: UGC
Ya ce wasu ‘yan Najeriya na ta cece-kuce a kan zargin rashawa da ake wa wasu manyan cibiyoyin gwamnatin tarayya da suka hada da NDDC, NSITF da EFCC.
KU KARANTA KUMA: DSS: Wasu fitattun 'yan Najeriya na shirin hargitsa kasar nan
Ya ce, “Wasu, musamman ‘yan adawa, suna fassara wannan ci gaban da alamun cewa gwamnatin ta yi sanyi a yaki da rashawa.
“A takaice, babban jam’iyyar adawa ta PDP ta yi amfani da wannan damar wurin kira ga shugaban kasa da ya yi murabu. Wannan kiran ba komai bane face bata baki.
“Bari in sake jaddadawa, yaki da rashawar gwamnatin nan yanzu aka fara. Tana nan daram babu gudu balle ja da baya.
“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi suna nagari a duniya a kan yaki da rashawa. Zai ci gaba da wannan jagoranci. Babu wanda ya isa ya bata masa suna duk da a karkashin mulkin PDP din aka yashe kasar nan.
“Duk wanda bai aminta da wannan yaki da rashawar ta shi ba, ya gwada mu ya gani ko zai yi nasara.”
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng