APC: Darajar Buhari ba za ta yi mana aiki a zaben 2023 ba - Udoedeghe
- John Udoedeghe ya gana da wasu Masoyan jam’iyyar APC
- ‘Dan siyasar ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar su tabbatar ana yi da su
- Sanata Udoedeghe ya ja-kunne da cewa guguwar Buhari ba za ta sake aiki ba
Sakataren APC na rikon-kwarya, Sanata John Udoedeghe ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyarsa da su yi kokari wajen ganin sun samu nasara a zabe mai zuwa.
John Udoedeghe ya ce zuwa babban zaben 2023, lokacin da mutane za su shige inuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya wuce.
Jaridar Punch ta rahoto jagoran jam’iyyar mai mulki ya na wannan kira a lokacin da ya zauna da wata kungiya ta magoya bayan APC a karkashin Frank Ossai.
An yi wannan zama ne a babban sakatariyar jam’iyyar APC da ke birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 22 ga watan Yuli, 2020.
KU KARANTA: 'Dan jam’iyya ya tafi kotu a kan zaben gwamnan jihar Edo

Asali: UGC
Udoedeghe ya ke cewa: “Dukkanku da ke siyasar kasa; ku tabbatar an cigaba da damawa da ku a mazabunku, da kananan hukumomi, da kuma jihohinku.”
A 2023 ne shugaba Buhari zai kammala wa’adinsa na shekaru takwas. Ana tunanin cewa APC ta na samun damar lashe zababbuka a matakai da-dama saboda sunansa.
Sanatan na jihar Edo ya gargadi magoya bayan jam’iyyar da cewa: “A zaben 2023, shugaba Muhammadu Buhari ba zai fito a cikin masu takara ba.”
‘Dan siyasar ya kuma shaidawa fusatattun ‘yan jam’iyyar APC cewa kwamitinsu na rikon kwarya a shirya ya ke da ya yi wa kowa adalci wajen dinke barakar da jam’iyyar ke fama da ita.
Kafin nan, shugaban tafiyar, Frank Ossai ya yi kira ga kwamitin rikon da ya duba aikin da Sanata Ken Nnamani ya taba yi domin kawo zaman lafiya a APC.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng