Malaman Musulunci Sun Gargaɗi ’Yan Najeriya kan Sayar da Ƙuri’a a Zaben 2027
- Majalisar Malaman Musulunci ta Najeriya ta buƙaci ’yan ƙasa su guji sayar da ƙuri’unsu a babban zaɓen 2027
- Majalisar ta buƙaci masu kaɗa ƙuri’a su zaɓi ’yan takara masu nagarta, ƙwarewa da kyakkyawan tarihin aiki maimakon la’akari da kuɗi ko muradun kansu
- Malaman sun kuma yi kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen magance matsalar tsaro, tallafa wa manoma da rage tsadar rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Majalisar Malaman Musulunci ta Najeriya ta buƙaci ’yan Najeriya da su guji sayar da ƙuri’unsu a babban zaɓen shekarar 2027, tana mai gargaɗin cewa zaɓen shugabanni marasa nagarta zai iya ƙara ta’azzara matsalolin ƙasar.
Majalisar ta buƙaci masu kaɗa ƙuri’a su zaɓi ’yan takara masu nagarta, ƙwarewa da kyakkyawan tarihin gudanar da ayyuka, maimakon yanke shawara bisa kuɗi ko muradun kansu.

Source: Facebook
Daily Trust ta ce an bayyana wannan kira ne a cikin sanarwar da majalisar ta fitar bayan taronta na shekara-shekara, wanda aka gudanar a zauren taro na Jama’atu Nasril Islam (JNI) da ke Kawo, Kaduna, a ranar 17 ga Oktoba.
Farfesa Muhammad Sadiq Abubakar, babban sakataren Majalisar Malaman Musulunci ta Najeriya, ne ya sanya wa sanarwar hannu.
Malamai sun ba yan Najeriya shawara
Malaman sun buƙaci ’yan Najeriya su yi nazari sosai kan ’yan takara kafin kaɗa ƙuri’a, suna mai cewa shawarar da suka yanke a rumfunan zaɓe za ta shafi rayuwarsu da kuma makomar ƙasar.
“Majalisar tana kira ga ’yan Najeriya da su fito su kaɗa ƙuri’a ga shugabannin da suka tabbatar da nagartarsu, kyawawan halayensu da ƙwarewarsu bisa la’akari da tarihin ayyukansu,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “Kada ’yan Najeriya su shiga siyasar kuɗi. Duk wanda ya ba su kuɗi, za su iya karɓa, amma su zaɓi ɗan takarar da ya dace, domin kuɗin tun farko na al’umma ne.”

Kara karanta wannan
2027: Shugaban INEC ya sanar da ma'aikatan hukumar abin da ba za su yarda da shi ba
Kira ga jam’iyyun siyasa
Majalisar ta kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa da su mutunta dokokin zaɓe tare da gudanar da harkokinsu cikin lumana, tana mai gargaɗin cewa ya kamata su guji duk wani mataki da zai iya haddasa tashin hankali ko rikici.
Ta buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da gudanar da sahihin zaɓe cikin ’yanci da adalci, tare da ɗaukar matakan hana duk wani abu da zai iya kawo cikas ga sahihancin zaɓen.

Source: Facebook
Malaman sun kuma jaddada cewa jam’iyyun siyasa da magoya bayansu su amince da sakamakon sahihin zaɓe, tare da barin duk wanda ya yi nasara ta hanyar gaskiya da bayyana gaskiya ya jagoranci ƙasar.
Wasu malamai sun juyawa Tinubu baya
Kun ji cewa malaman addinin Musulunci daga jihohin Arewa 19 su gudanar da taro na musamman domin nuna adawa da tazarcen shugaba Bola Tinubu.
Sun bayyana cewa sun yi taron ne bayan gudanar da cikakken nazari kan yadda shugaban kasar ya tafiyar da Najeriya daga 2023 zuwa yau.
Asali: Legit.ng
