Nesa Ta Zo Kusa: CDCFIB Za Ta Sake Bude Shafin Daukar Ma'aikata a Hukumomi 4 a Najeriya
- Hukumar CDCFIB za ta sake buɗe shafin dauka aikin ta daga 28 ga Oktoba zuwa 13 ga watan Nuwamba, 2026
- Za a bude shafin ne domin waɗanda suka tsallake matakan tantancewa su duba matsayinsu kafin tsallakawa zuwa mataki na gaba
- Duk wanda ya tsallake zai samu lambar da zai yi amfani da ita wajen gwajin ta'amali da miyagun ƙwayoyi a ofishin NDLEA da ke jiharsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Kula da Ma’aikatan Tsaron Farar Hula ta sibil defens, Gidan Yari, Kashe Gobara da Shige da Fice (CDCFIB) ta ce za ta sake buɗe shafinta na ɗaukar ma’aikata daga ranar 28 ga Oktoba zuwa 13 ga Nuwamba, 2026.
Ta bayyana cewa za ta bude shafin ne domin wadanda suka kammala gwajin lafiya, tattaunawar baki da sauran matakai su duba matsayin neman aikinsu a hukumomi 4.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Yan bindiga sun rutsa shugaban matasan APC da matarsa a cikin gida

Source: Twitter
Dalilin sake bude shafin CDCFIB
A rahoton Leadership, CDCFIB ta ce duk mutanen da suka tsallake wadannan matakai za su samu lambobin da za su yi amfani da su wajen gwajin ta'amali da miyagun ƙwayoyi.
Wadanda za su duba idan an bude shafin sun hada da masu neman aikin sibil defens (NSCDC, gandurorbobi, jami'an hukumar kashe gobara da na hukumar shige da fice (NIS)
Sake buɗe shafin na daga cikin matakan ƙarshe na aikin ɗaukar ma’aikatan da ake gudanarwa a yanzu. Ana buƙatar wadanda suka cike su kammala gwajin shaye-shaye kafin su karɓi takardun kama aiki.
Sakataren hukumar, Manjo-Janar A.M. Jibril (mai ritaya), ne ya bayyana hakan yayin taron kwamitin gudanarwa karo na biyu na wannan shekara.
Ya ce sake buɗe shafin ba sabon shirin ɗaukar ma’aikata ba ne, illa ci gaba da aikin da aka fara.
A cewarsa, ana sa ran wadanda suka nema da suka kai matakin gwajin baka za su shiga shafin neman aikin na hukumar a lokacin da aka ware domin tabbatar da matsayinsu da karbar lambobin da ake buƙata don gwajin miyagun ƙwayoyi

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: An gano masu shirya kai farmaki kan matasan da za su y aikin zaɓen 2027
Ya bayyana cewa aikin na daga cikin shirin gwamnatin tarayya na ɗaukar ma’aikata 30,000 zuwa hukumomin tsaro huɗu na ƙasar, a matsayin matakin farko na babban shirin ɗaukar ma’aikata 120,000.
Yadda za a yi gwajin shaye-shaye
Jibrin ya ce wadanda suka cancanta za su je ofishin Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) da ke jihohinsu domin yin gwajin da ake buƙata.
Ya jaddada cewa gwajin zai kasance kyauta ga duk wadan da suka cancanta, domin gwamnatin tarayya ce za ta ɗauki nauyin kuɗin gudanar da shi.

Source: Twitter
Ya bayyana cewa abin da ake buƙata daga ’yan takarar shi ne su shiga shafin neman aikin, su samo lambobin gwajinsu, sannan su je ofisoshin NDLEA da aka ware domin bayar da samfurin da za a yi amfani da shi wajen gwajin.
Ya kuma bayyana cewa za a fitar da sakamakon gwajin nan take, domin waɗanda suka cika sharuɗɗan su ci gaba da sauran matakan ɗaukar aikin.
An bude shafin daukar ma'aikatan zabe
Kun ji cewa hukumar INEC ta buɗe shafin neman aikin ma'aikatan wucin gadi da za su taimaka wajen gudanar da babban zaɓen 2027.
Hukumar ta ce aikin neman ma'aikatan zai gudana ne ta tsarin daukar ma'aikata na INEC , inda ƴan Najeriya da suka cika sharuɗɗan za su iya neman aikin a jihohin ƙasar.
Asali: Legit.ng