Yanzu: Shugaba Buhari ya sauka a birnin Bamako
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bisa jagorancin shugaban kasar jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou, ya sauka a Bamako, babban birnin kasar Mali.
Legit.ng ta wallafa rahoton cewa Buhari zai tuntubi sauran shugabannin kasashen nahiyar Afrika a kan yadda za a samu zaman lafiya mai dorewa a kasar Mali mai fama da rigingimu daban - daban.
Buhari ya bayyana hakan ne ranar Talata bayan karbar rahoto daga wurin wakilin zaman lafiya na musamman da aka tura kasar Mali, tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan.
A cewar wani jawabi da kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya fitar a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja, ya ce Jonathan ya samu rakiyar shugaban kungiyar ECOWAS, Mista Jean-Claude Kassi Brou.
"Za mu tattauna da shugaban kasar Nijar, wanda shine ciyaman na ECOWAS, domin ya gabatar da mana jawabi, daga nan kuma za mu san menene mafita," a cewar shugaba Buhari.
A cikin tawagar shugaba Buhari da ta isa kasar Mali domin tattauna yadda za a samu zaman lafiya akwai tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Zanga - zangar neman shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita, ya sauka daga kan mulkinsa duk da yana da sauran shekaru uku a cikin biyar na zangon mulkinsa na biyu, ta rikide zuwa rikici.
Wata kungiyar 'yan tawaye mai suna 'M5' ta bukaci a rushe kotunan kasar Mali da kundin tsarin mulki ya kafasu, sannan shugaba Keita ya yi murabus matukar ana bukatar samun lafiya a kasar.
DUBA WANNAN: Buhari ya amince da rabawa matasa tallafin jari na naira biliyan N75
Rikici ya barke bayan kotunan kasar Mali sun kwace kujerun mambobin majalisa 31 tare da mikasu zuwa hannun wasu 'yan takara da aka bayyana sun fadi bayan kada kuri'a.
Kungiyar 'M5' ta yi zargin cewa kotunan sun aikata hakan ne bisa umarnin shugaba Keita.
Kungiyar ECOWAS ta yanke shawarar shiga rikicin kasar Mali bayan al'amura sun kara dagulewa a 'yan kwanakin baya bayan nan sakamakon kashe wasu masu zanga-zanga da jami'an tsaro su ka yi a ranar 10 ga watan Yuli.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng