Magu: Ma’aikatu da Fadar Shugaban kasa aka yi wa gwanjon kayan sata

Magu: Ma’aikatu da Fadar Shugaban kasa aka yi wa gwanjon kayan sata

Tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya ce wasu daga cikin motocin da ya karbe daga hannun barayi su na hannun ma’aikatun gwamnati da fadar shugaban kasa.

Ibrahim Magu ya bayyana cewa EFCC ta yi wa sabuwar ma’aikatar bada agaji da kuma fadar shugaban Najeriya, da hukumar FIRS da wasu ma’aikatu gwanjon motocin satan.

Jaridar Punch ta rahoto Magu ya na cewa hukumar EFCC ba ta kammala karbar kudin motocin daga hannun wasu ma’aikatun ba, amma an tsara yadda za a cire bashin daga kasonsu.

Mista Magu ya bayyana wannan ne a wata wasika mai taken 'Re: Alleged Case of Conspiracy, Enrichment, Abuse of Public Office and Other Infractions' da ya aikawa kwamitin Ayo Salami.

Mukaddashin na EFCC wanda aka dakatar kwanaki ya wanke kansa daga zargin da kwamitin shugaban kasar ya ke yi masa na azurta kansa da kudi N550bn da dukiyar al’umma.

A martaninsa, Magu ya fayyace yadda har yanzu wasu motoci 450 da EFCC ta karbe daga hannun barayi su ke zaune ba tare da an saida su ba duk da hukumar ta samu izni daga shugaban kasa.

KU KARANTA: Magu ya rabawa Abokansa gidajen da ya karbo daga barayi - Fayose

Magu: Ma’aikatu da Fadar Shugaban kasa aka yi wa gwanjon kayan sata
Ibrahim Magu da Shugaban kasa
Source: Facebook

Wadannan motoci su na garuruwan Abuja da Legas ne kamar yadda Ibrahim Magu ya bayyana. Akasin zargin da ake yi na cewa Magu ya rabawa na-kusa da shi motoci da gidaje.

Haka zalika a game da batun gidajen da EFCC ta karbe har abada daga barayin gwamnati, Magu ya ce an saidawa wasu hukumomi da ma’aikatun gwamnati wadannan gidaje.

Daga cikin ma’aikatun da aka ba wadannan gidaje akwai: VON, sabuwar hukumar NEDC da aka kafa domin cigaban Arewa maso gabas, da kuma ma’aikatar fansho ta PTAD.

EFCC ta bada hayar gidajen da har yanzu ake kotu a kansu kafin a kammala shari’a. Wadanda su ka karbi hayar gidajen sun hada da ma’ikatar kudi, sojojin Najeriya, FRC, NIDCOM, da FAAN.

Sauran ma’aikatun da su ka bukaci EFCC ta ba su hayar gidajen sata su ne; NHRC da NCAC kamar yadda Magu ya bayyana. Wasu gidajen kuma sun zama wurin killace masu COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel