Yanzu-yanzu: Mutum 8 sun rasa rayukansu a sabon rikicin Zangon Kataf

Yanzu-yanzu: Mutum 8 sun rasa rayukansu a sabon rikicin Zangon Kataf

An tabbatar da mutuwar mutane 7 a sabon rikicin da ya barke a kauyen Gan da ke zangon Kataf a jihar Kaduna.

Shugaban kungiyar kiristoci ta kasa, reshen karamar hukumar Zangon Kataf, Fasto Isaac Ango Manama ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar Leadership a ranar Talata.

Ya ce maharan da suka kai farmaki kauyen da misalin karfe 7:00 na yamma sannan suka fara harbe-harbe sun wuce mutum 50.

Ya ce a halin yanzu an samu gawawwakin mutum takwas kuma suna babban asibitin Zo kwa yayin da wasu kauyawan suka bace.

"Ina kira ga jama'a da su kira wakilansu da basu jajanta musu ba a kan wannan kaddarar.

"Har yanzu babu dan majalisar jihar da ya ziyarci sansanin, hakan nuni ne da cewa basu damu da damuwarmu ba," in ji shi.

Yanzu-yanzu: Mutum 8 sun rasa rayukansu a sabon rikicin Zangon Kataf
Yanzu-yanzu: Mutum 8 sun rasa rayukansu a sabon rikicin Zangon Kataf Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Sakataren sansanin 'yan gudun hijira na Zonkwa, Ezekiel James ya bayyana cewa ya yi wa mutum 559 rijista da suka tsere daga kauyukan da ke da makwabtaka da su.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya shiga ganawar sirri da Jonathan

Ya kara da cewa sansanin na matukar bukatar magunguna da ababen amfani.

Ya yi kira ga masu hali da su tallafa wa wadannan 'yan gudun hijira.

A wani labari na daban, Shugaban sojojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya je fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke Abuja a ranar Litinin.

Buratai ya je bayyanawa shugaban kasar inda aka kwana a wurin yaki da rashin tsaro.

A yayin ganawa da manema labarai bayan taron, ya ce domin shawo kan wannan matsalar, dole ne dukkan 'yan Najeriya su hada kai wurin yaki da ta'addanci.

Ya ce duk da ta'addanci sabon abu ne a kasar nan, rashin tsaro ya dade amma abu mafi muhimmanci shine yadda za a shawo kan shi.

Kamar yadda yace, duk da cewar akwai kalubale wajen shawo kan matsalar, hakan ba yana nufin masu kula da tsaron basa kokarin bane.

Buratai ya tabbatar da cewa ya je fadar shugaban kasar ne don sanar da shi nasarorin da aka samu a cikin aikin da aka bashi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel