FG ta fara gwajin sabbin jiragen kasa da ta sayo daga China (Bidiyo)

FG ta fara gwajin sabbin jiragen kasa da ta sayo daga China (Bidiyo)

Gwamnatin tarayya ta fara gwajin sabbin jiragen kasa da ta sayo daga kasar China, kamar yadda ministan sufuri, Rotimi Amaechi, sanar da yammacin yau, Juma'a.

Da ya ke sanar da hakan a shafinsa na tuwita, Amaechi ya bayyana cewa an fara gwajin sabbin jiragen a kan sabbin titunan jirgin kasa da aka gina daga Itakpe zuwa Warri.

Jama'a da dama sun yabawa kokarin Amaechi a yayin da suke bayyana ra'ayinsu a kan faifan bidiyon sabbin jiragen da ya wallafa a shafinsa na tuwita.

Kimanin watanni uku kenan da dukumar jiragen kasan Najeriya (NRC) ta dakatar da jigilar fasinjoji a jiragenta da ke sagaraftu a tsakanin Abuja zuwa Kaduna, Legas zuwa Ibadan da sauran sassan tarayya.

Mataimakin kakakin hukumar, Yakubu Mahmoud, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Asabar, 21 ga Maris, 2020.

Yace “Hukumar jiragen kasan Najeriya ta yanke shawarar dakatad da jigilar fasinjoji fari daga ranar Litinin 23 ga Maris, 2020.“

An yanke shawarar ne sakamakon yaduwar cutar Coronavirus“ “Za a sanar da fasinjoji duk lokacin da aka canza shawara.“

Sai dai, har yanzu NRC ba ta sanar da dawowar aikin jigilar fasinjoji a jiragen kasa ba duk da jiragen sama sun fara jigilar fasinjoji a iya cikin gida.

FG ta fara gwajin sabbin jiragen kasa da ta sayo daga China (Bidiyo)
Amaechi
Asali: UGC

Kimanin wata guda kenan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da biyan N123 biliyan don aikin titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano.

Amaechi ya bayyana cewa akwai yuwuwar a fara aikin titin jirgin kasan zuwa karshen watan Augusta.

Aikin, wanda gwamnatin kasar China ta dauka nauyi zai ci $5.3 biliyan.

Kamfanin China 'Civil Engineering and Construction Corporation' ne zai yi aikin.

DUBA WANNAN: Nan bada dadewa ba za a rasa ma su karfin gwuiwar yaki da cin hanci - Osinbajo

Da ya ke sanar da hakan a tattaunawar da aka yi da shi a gidan talabijin din Channels a ranar Damokaradiyya, Amaechi ya jinjinawa gwamnatin kasar China wacce yace tana matukar taimako wurin mayar da titunan jiragen kasa na tarayya zuwa na zamani.

Ya ce majalisar zartarwa ta tarayya (NEC) ta amince da bude asusun da za a dinga saka ribar da aka samu daga ayyukan jiragen kasan don biyan gwamnatin kasar China.

A cewar ministan, lokacin da jirgin kasan ya fara aiki, gwamnati na asarar N46 miliyan a kowanne wata, amma a yanzu ana samun ribar N109 miliyan zuwa N110 miliyan a kowanne wata.

Amaechi ya kara da cewa, a lokacin da jiragen kasan Ibadan zuwa Kano za su fara aiki tare da taragon daukar kaya, za a samu riba mai tarin yawa da za ta kawo sassauci wurin biyan bashin da aka ci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel