Ayyuka 774,000: Bayan sabani da 'yan majalisa, Buhari ya goyi bayan ministansa

Ayyuka 774,000: Bayan sabani da 'yan majalisa, Buhari ya goyi bayan ministansa

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin daukar ma’aikta na musamman da majalisar dokoki ta dakatar.

Gwamnatin ta sanar da kaddamar da shirin ta shafinta na Twitter a ranar Talata, 14 ga watan Yuli.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da shirin wanda ma’aikatar kwadago ke jagorantar, daga cikin matakan rage radadin annobar korona.

Za a dauki mutum 1,000 daga kowani karamar hukuma 774 da ke kasar, sannan kwamitocin jiha za su kula da shirin.

An kaddamar da kwamitocin zaben ma’aikatan na jiha kuka sun fara aiki,” cewar gwamnatin tarayya ta shafinta na Twitter.

Keyamo ya yi cacar baki da majalisar dattawa a kan cewar su za su tsara yadda daukar aikin za ta kasance.

Kwamitin majalisar tarayya a kan kwadago ya dakatar da fara diban aikin sakamakon hatsaniyar da ta shiga tsakaninsu da karamin ministan.

Ayyuka 774,000: Bayan hargitsi da 'yan majalisa, Buhari ya goyi bayan ministansa
Ayyuka 774,000: Bayan hargitsi da 'yan majalisa, Buhari ya goyi bayan ministansa Hoto: The Cable
Asali: UGC

A wani taro da suka yi a watan Yuni, mambobin kwamitin sun kusa bai wa hammata iska tsakaninsu da ministan inda daga bisani suka koreshi daga majalisar.

Amma Keyamo ya zargesu da yunkurin kwace daukar aikin tare da son amshe guraben don amfanin kansu da makusantansu.

Ya kara da zargar 'yan majalisar da kokarin kalubalantar hukuncin shugaban kasar.

Ya ce 'yan majalisar sun dauki mataki da ya fi karfinsu.

The Cable ta gano cewa Keyamo ya samu ganawa da shugaban kasa inda ya bayyana mishi abinda ya faru a majalisar a kan shirin.

Shugaban kasar ya matukar fusata da yadda 'yan majalisar ke son yin katsalandan a al'amarin da ya shafi masu zartarwa.

Ya bukaci ministan da ya ci gaba da shirin kuma ya tabbatar da an yi shi bisa tsarin da ya dace na shari'a.

Ya kara da bukatar darakta janar na NDE da ya tsayar da duk wani tsari na daban a kan shirin wanda yake yi tare da kwamitin majalisar tarayya.

An kuma tattaro cewa, ministan shari'a, Abubakar Malami, ya rubuta wasika ga 'yan majalisar da su kiyaye iyakokinsu.

KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun damke dattijo mai shekaru 48 da ya yi wa yarinya fyade

A baya Legit.ng ta rahoto cewa za a bai wa gwamnonin jihohi, 'yan majalisar tarayya da ministoci gurbi na musamman a ayyuka 774,000 da gwamnatin tarayya za ta dauka.

Kwamitin zaben ma'aikatan ne ya bayyana hakan a jiya Laraba yayin sanar da yadda daukar wadanda za su ci moriyar shirin za ta kama, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Shugaban kwamitin a jihar Bauchi, Sanusi Aliyu Kunde, ya sanar da hakan yayin rantsar da kwamitin na jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng.

Asali: Legit.ng

Online view pixel