Zargin fasa bututu: Nunieh ta je asibiti ayi mata allurar natsuwa - Akpabio

Zargin fasa bututu: Nunieh ta je asibiti ayi mata allurar natsuwa - Akpabio

Ministan harkokin Neja-Delta, Sanata Godswill Akpabio ya karyata zargin da ake yi masa na cewa ya bada umarnin a fasa wasu batutun mai a Najeriya.

Tsohuwar shugabar hukumar NDDC, Dr. Gbene Joy Nunieh ta jefi ministan da wannan zargi a fallasar da ta fito ta na yi a ranar Juma’a, 10 ga watan Yuli, 2020.

Da ta ke bayani a gaban ‘yan jarida bayan ta halarci wata zama da aka yi a majalisar dattawa, Nunieh ta ce ministan ya bada umarnin a fasa bututu saboda bata mata suna.

“An fasa wasu bututun mai saboda kurum a tsige ni. Minista mai-ci zai iya zuwa ya fasa bututu a Neja-Delta.

Ta ce: Mutumin da ya taba rike kujerar Gwamna, ya zama Sanata, kuma Minista, ya je ya fasa bututu.”

Da aka yi hira da ministan a gidan talabijin, ya musanya wadannan zargi masu karfi, a maimakon haka ya bayyana cewa Dr. Gbene Joy Nunieh ta na larura.

A cewar Sanata Akpabio, Gbene Joy Nunieh ta na fama da matsalar fushi, don haka ya bada shawarar ta tafi asibiti domin ayi mata alluran da za su natsar da ita.

KU KARANTA: Abin da na yi wa Akpabio da ya yi mani maganar banza - Nunieh

Zargin fasa bututu: Nunieh ta je asibiti ayi mata allurar natsuwa - Akpabio
Dr. Joy Nunieh
Asali: Twitter

Godswill Akpabio ya bayyana cewa za a iya tabbatar da matsalar fushin Gbene Joy Nunieh wanda ta rike NDDC na rikon kwarya daga wurin mazajen da ta rika aure a baya.

Mai girma ministan ya ce Joy Nunieh ta auri mazaje har hudu a baya. Ministan ya yi watsi da zargin da ake yi masa, ya koma magana a game da rayuwar wannan mata.

“Bari in yi bayani game da wannan, tsohuwar shugabar NDDC da aka ambata, duk da karfin zargin, ina ma ace za ta tafi asibiti, ta samu ganin likita, sai ayi mata allura domin ta natsu.”

Ya kara da cewa: “Ba cewa na ke yi wani abu na damun ta ba, abin da na ke cewa shi ne akwai matsala tattare da fushinta. Babu bukatar a tambaye ni, a tambayi sauran maza hudu da ta aura.”

Ministan ya nemi a kawo mazajen da Joy Nunieh ta aura a gaban gidan talabijin, ayi masu tambaya game da dabi’ar ta ta. Har yanzu Nunieh ba ta tanka wannan batu ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel