Katsina: 'Yan bindiga sun kai hari a daidai lokacin da Buratai ke kaddamar da sabon atisaye

Katsina: 'Yan bindiga sun kai hari a daidai lokacin da Buratai ke kaddamar da sabon atisaye

Babban hafsan rundunar sojojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, bisa rakiyar dumbin dakarun soji, ya sake kaddamar da wani atisaye mai taken ,Ofireshon Sahel Sanity, a ranar Litinin domin magance aiyukan 'yan bindiga a yankin arewa ma so yamma.

Yayin kaddamar da sabon atisayen a karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina, Buratai ya ce an kaddamar da sabon atisayen da sauran wasu a baya domin dawo da zaman lafiya a jihohin yankin arewa ma so yamma da 'yan bindiga su ka addaba.

"Rundunar sojin Najeriya za ta gudanar da atisayen Sahel Sanity tare da hadin gwuiwar sauran hukumomin tsaro da suka hada da rundunar 'yan sanda, jami'an tsaron farin kaya (DSS) da gwamnatin.

"A shirye mu ke mu kawar da 'yan bindiga, satar shanu da sauran wasu aiyukan ta'addanci a yankin arewa ma so yamma da arewa ta tsakiya," a cewar Buratai.

Sai dai, a yayin da Buratai ke kaddamar da wannan atisaye, wasu 'yan bindiga sun kai hari kauyen Yar Gamji mai nisan kilomita 150 daga karamar hukumar Batsari tare da kashe manoma 30 da ke aiki a gonakinsu.

'Yan bindigar, kimanin su 200, sun dira kauyen a kan babura da misalin karfe 10:30 na safiyar ranar Litinin.

Mazauna kauyen sun sanar da jami'an tsaro halin da ake ciki kuma an turo dakarun soji domin bayar da gajin gaggawa.

Katsina: 'Yan bindiga sun kai hari a daidai lokacin da Buratai ke kaddamar da sabon atisaye
T. Y Buratai
Asali: UGC

'Yan bindigar sun gudu zuwa cikin dazukan da suka fito bayan sun dan fafata musayar wuta da jami'an tsaro.

DUBA WANNAN: Kamar a fim: Yadda jiragen yakin sojoji suka dinga ruwan wuta a wasu maboyar Boko Haram

Jaridar Daily Trus ta rawaito cewa ya zuwa wannan mako da mu ke ciki, akwai mutane 6,914 a sasanin 'yan gudun hijira guda uku da ke Faskari, Dandume da Batsari.

Yawaitar hare - haren 'yan bindiga a yankin arewa maso yamma ya tilastawa jama'a da dama guduwa zuwa kasar Nijar.

A ranar Litinin ne Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta sanar da cewa ta kashe dumbin mayakan kungiyar Boko Haram.

A kashe mayakan ne yayin wani luguden wuta da jiragen yaki na rundunar NAF suka yi a sansanin mayakan da ke Parisu da Bula Bello a dajin Sambisa da ke jihar Borno.

Manjo Janar John Enenche, shugaban sashen yada labaran atisayen rundunar soji, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar da safiyar ranar Litinin.

A cewar Janar Enenche, rundunar soji ta kai harin ne; "ranar 3 ga watan Yuli a cigaba da atisayen rundunar soji na karasa murkushe mayakan kungiyar Boko Haram bayan samun bayanan sirri a kan wasu sansani da mayakan ke buya.

"Rundunar soji ta aika jiragenta na yaki bayan tabbatar da cewa mayakan suna buya a sansani. Jiragen sun yi luguden wuta, sun saki bamabamai da makamai ma su linzami a sansanin.

"Dumbin mayakan kungiyar sun mutu, sannan an lalata sansaninsu yayin ruwan wutar da jiragen suka yi," a cewar wani bangare na jawabin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel