Labari da dumi: Mataimakin Akeredolu ya maka majalisar jihar Ondo a kotu

Labari da dumi: Mataimakin Akeredolu ya maka majalisar jihar Ondo a kotu

- Rikici da barakar da ke tsakanin Gwamna Rotimi Akeredolu da mataimakinsa Agboola Ajayi ya dauki wani sabon samfur

- Mataimakin gwamnan na jihar Ondo ya maka majalisar jihar a gaban kotu sakamakon zargin yunkurin tsigesa daga kujerarsa

- An zargi majalisar da yunkurin tsige Agboola bayan sauya sheka da yayi zuwa jam'iyyar PDP inda yake neman kujerar gwamnan

A tsaka da rikicin siyasa, hargitsi tsakanin mataimakin gwamnan jihar Ondo, Ajayi Agboola da ubangidansa, Rotimi Akeredolu na kara kamari.

A wani rahoton da jaridar Premium Times ta fitar, mataimakin gwamnan ya maka majalisar jihar a gaban kotu sakamakon zarginsu da yake da kokarin tsigesa.

Ajayi yace ya yanke hukuncin mika bukatarsa gaban kotu don hana majalisar kokarin tsigesa daga kujerarsa bayan barin jam'iyyar APC da yayi zuwa ta PDP.

A ranar Litinin, lauyan mataimakin gwamnan, I. Olatoke ya shigar da kara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda suke bukatar dakatar da yunkurin tsigesa tare da jaddada hakkinsa na 'yancin mu'amala.

Idan za a tuna, Agboola ta bakin hadiminsa Allen Sowore, ya zargi shirin tsigesa da ake yi. Ya ce gwamnan ya bai wa 'yan majalisa 19 daga cikin 23 N10 miliyan don su goyi bayan tsigesa.

KU KARANTA KUMA: Zaben gwamna: PDP ta karbi sabbin 'yan adawa 106 a jihar Edo

Amma kuma, Gwamna Akeredolu ya bayyana ikirarin Agboola a matsayin karya zalla wacce ta rasa shaida.

Akeredolu ya ce ba zai gina alkawurran yakin neman zabensa ba a kan karairayi marasa tushe da makama.

A baya mun ji cewa Jam'iyyar APC ta tsara yadda za ta dawo da zaman lafiya a tsakanin 'ya'yanta don samun damar lashe zabukan jihohin Edo da Ondo da ke karatowa.

Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya ce jam'iyyar za ta hanzarta sasanta 'ya'yanta a duk fadin kasar nan don dawo da zaman lafiya tare da lumana, jaridar The Nation ta ruwaito.

A ranar Litinin, 29 ga watan Yuni, jam'iyyar ta kafa kwamitin sasanci a babban ofishin jam'iyyar da ke Abuja.

Ta fidda tsari shida wanda za ta yi amfani da su wurin gyara zaman jam'iyyar a taron rantsarwar da aka yi wa 'yan kwamitin rikon kwaryar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng