Nasara daga Allah: Matan babban kwamandan Boko Haram sun shiga hannu, an kashe mayaka 75

Nasara daga Allah: Matan babban kwamandan Boko Haram sun shiga hannu, an kashe mayaka 75

- Dakarun Operation Lafiya Dole sun halaka mayakan Boko Haram 75 tare da samo miyagun makamai daga wurinsu a yankin arewa maso gabas

- Mayakan na Boko Haram su tarar da ajalinsu ne yayin arangama 17 da suka yi da dakarun sojin daga ranar 1 ga watan Yuni zuwa 30 ga watan Yuni

- An kuma kama matan kwamandan Boko Haram da ke Gajingi a karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa su biyu

Rundunar Operation Lafiya Dole ta kashe mayakan Boko Haram 75 tare da samo miyagun makamai daga wurinsu a yankin arewa maso gabas.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche, ya tabbatar da aukuwar hakan ta wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi.

Kamar yadda yace, an kashe mayakan ne sakamakon harin da dakarun sojin suka kai wanda yasa mayakan suka mutu tare da samo wasu makamansu.

Enenche ya ce mayakan Boko Haram din su tarar da ajalinsu ne yayin arangama 17 da suka yi da dakarun sojin daga ranar 1 ga watan Yuni zuwa 30 ga watan Yuni.

Nasara daga Allah: Matan babban kwamandan Boko Haram sun shiga hannu, an kashe mayaka 75
Nasara daga Allah: Matan babban kwamandan Boko Haram sun shiga hannu, an kashe mayaka 75 Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

"Ana samun manyan nasarori na murkushe mayakan ta'addancin da suka addabi yankin arewa maso gabas. An samu halaka wasu, an samu makamai yayin da wasu daga ciki suka mika wuya ga dakarun sojin.

"A kokarin dakarun sojin na kawo karshen Boko Haram, dakarun rundunar Operation Lafiya Dole sun kai hari 17 ga mayakan tare da kashe 75 daga ciki," takardar tace.

Daga cikin makaman da aka samo akwai bindigar baro jiragen sama 1, bindiga kirar AK 47 13, bindigar toka 21 da sauransu.

Akwai bama-baman masu linazami, harsasai 1018 da kuma tutocin Boko Haram 2.

Mai magana da yawun rundunar ya yi bayanin cewa an samu motar yaki daya, motar dasa bam daya, mota kirar Toyota Starlet daya da sauransu, Channels TV ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Harbo jirgin UN: Majalisar dinkin duniya ta bukaci bincike da hukunci

Ya yi jajen yadda daya daga cikin dakarun su ya rasa ransa yayin da wasu suka samu raunika.

An ceto mutum 35, daga ciki 18 mata ne sai kanana yara 16 da magidanci daya.

A yayin karin bayani, Enenche ya ce hudu daga cikin 'yan ta'addan da suka hada da mata biyu sun shiga hannu. An gano cewa matan kwamandan Boko Haram ne da ke Gajingi a karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel